Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ba ta kullaci Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ba, dangane da sakamakon zaben gwamnan Jihar Bayelsa da aka gudanar ranar Asabar da ta wuce.
Sakataren Yada Labarai na PDP, Kola Ologbondiyan ne ya sanar da haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, jiya Laraba a Abuja.
An samu yaduwar rahotanni da ke nuna cewa mai yiwuwa PDP ta hukunta Jonathan bisa zargin yankan-bayan da ya yi wa dan takarar gwamna na PDP, abin da jama’a ke ganin cewa dalilin hakan ne ya sa APC ta yi nasara a zaben gwamnan jihar Bayelsa, wanda aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.
Duk da ana zargin Jonathan ya mara wa APC baya, Ologbondiyan ya shaida wa ’yan jarida cewa a taron da masu ruwa da tsakin PDP suka yi jiya,ba a ma tattauna batun Jonathan a wurin ba.
“Ya kamata kusan yadda tsarin jam’iyyar PDP ya ke. Idan babu batun tattauna wani batu a cikin ajandar taron mu, to fa ba za a tattauna shi idan an zauna taron ba.
“Saboda haka, mu dai har zuwa yanzu din nan da na ke magana da ku, babu wani batun Jonathan da aka kawo a gaban uwar jam’iyyar PDP.
Daga nan sai ya ce abin da aka tattauna a wurin taron shi ne batun zaben Bayelsa da Kogi. Kuma shugaban jam’iyya Uche Secondus zai yi wa manema labarai jawabi a gobe Alhamis.
“A kan wadannan zabuka, tuni muka yanke shawarar garzayawa kotu. Sannan kuma akwai wani mataki da aka dauka, amma shi Shugaban Jama’iyya Secondus ne zai yi muku jawabi a kan batun.