Babban Joji ne ya umarci Alkali ya ci gaba da Tsare dalibin jami’a Yahuza -Inji dan majalisar Kano

0

A wani faifan radiyo da aka dauka a wani hira da dan majalisar jihar Kano dake wakiltar Madobi, an ji shi kakara ya bugun kirji yana cewa Ko sarkin Kano Sanusi ba zai iya saka shi abu yayi ba.

A wannan faifai an ji Honarabul Isma’ila yana cewa babban jojin jihar Kano ne ya umarce Alkalin dake sauraren karar da ya shigar game da cin fuskar da yake zargin dalibi Yahuza dake karatu a jami’ar Bayero da yayi masa da ya ci gaba da tsare shi a gidan kaso har zuwa wani lokaci.

” Duk Madobi indan ana batun ga wane shegen kansa ne, wanda a baya zai iya yin duk abin da yaga dama kowa dai ya san haka yake amma wallahi tallahi babu mutum da zai yi mun haka ya ce zai ci lafiya.Wallahi da daga kaina ba zai kara ba.

” Saboda haka nake ganin wannan itace hanya mafi sauki tun da mu musulmai ne domin duk abin da ka aikata ka san kana da sakamako.Kuma wannan abun da na yi na tabbata har ga Allah ban zallunci Yahuza ba.

” Misali duk Kazafi-Kazafi da Yahuza ya ambato idan bulalla za a yi masa bulala nawa zai sha idan aka kwantar da shi?Sannan idan zan kai shi kotu na shigar da kara nawa Yahuza zai kashe domin bashi da yadda zai yi ya biya na.

” Ku saurari abin da nake gaya muku game da abin da Yahuza ya yi domin a rayuwa wani zai ga cewa an yi amfani da girmar kujeran sa ne domin ya dane Yahuza.Amma ni na sani ko bana kan kujera, ni ba sa’an Yahuza bane domin ko babu komai ka tursasa ni zan iya fito maka da miliyan 50 zuwa 100. Amma Yahuza idan ka matsa masa akan 100,000 sai duniya ta ji. Ka ga ko a nan ma na fi karfin sa.

” Duk wani da ake tunanin wani babu wanda bai kira ni ba irin su Abdullahi Abass…, Domin akan wannan abun saida cif joji ya kira ni mun yi zama da Cif Joji akan wannan ya kuma kira Alkali ya bashi Umarnin ya ci gaba da daure shi.

Idan ba a manta ba, har yanzu dai matashin dalibin nan dake karatu a Jami’ar Bayero dake Kano, Yahuza Tijjani na nan tsare a gidan kaso a dalilin wai ya yi rubutun suka ga wani dan majalisa dake wakiltar Madobi a majalisar jihar Kano.

Dan majalisar, Kabiru Ismaila ya zargi Yahuza da yin rubutun suka da cin fuska akan sa a shafinsa na Facebook.

Honarabul Ismaila bai yi wata-wata ba sai ya yi amfani da karfin kujerar sa ya sa ‘yan sanda suka cafke dalibi Yahuza.

Bayan yan kwanaki da yayi tsare a wurin ‘yan sanda sai aka kai shi kotun dake unguwar (No Mans Land) dake Karamar hukumar Fage, daga nan sai alkali ya daure Yahuza.

‘Yan uwan Yahuza da suka zanta da PREMIUM TIMES sun bayyana cewa suna kokarin ganin an sako Yahuza don ya koma makaranta amma abin ya citura domin ko daga baya da suka samu alkalin da ya yanke hukuncin tun a farko ya fadi musu cewa an maida shari’ar ofishin Antoni Janar din jihar.

” Mun yi ta jigila zuwa ma’aikatar shari’a ta jihar amma a duk sa’adda muka je sai a hana mu ganin kwamishinan. Babban abi da muke tsoro shine kada a sallameshi daga makaranta domin domin ya shafe tsawon lokaci baya zuwa karatu.

An ce Yahuza ya maida da martani ne ga wasu dake goyon bayan shi honorabul Ismaila a Facebook inda ya ce ” gwanin nasu ma bai iya lissafi ba sannan ko makaranta bai yi ba.” A tsakaninsu can a Facebook, amma shine wannan dan majalisar yayi amfani da dama da karfin kujerar sa ya a daure shi .

Kungiyar daliban Najeriya reshen jihar Kano sun yo tattaki bar zuwa ga wannan dan majalisa suka roke shi amma ya ki amincewa da ya bada da dama a sake shi.

PREMIUM TIMES ta samu ji daga bakin shi honorabul Kabir Ismaila, domin jin ko akwai dalilin da ya sa yaki sairaren jama’a da tausaya wa wannan dalibi.

” Yahuza ya ci mini mutunci ne ya. Da naga ba zan iya hakuri ko kuma in yi wani abu da zai saba wa doka ba sai na kai kara ga hukuma domin abi min hakki na. Amma babi wanda zai iya hakura da irin kalaman da wannan yayi a kai na.

Share.

game da Author