Dan taratsin mai horas da ‘yan wasa, Jose Mourinho, ya karbi kwangilar koyar da ’yan wasan Tottenham FC da ke Londo, inda aka dankara masa albashin da ya bai wa duniyar kwallon kafa al’ajabi.
Tottenham dai ita ce kungiyar kwallon kafa ta 9 da Mourinho ya zama kociya.
An rattaba yarjejeniyar rika biyan Mourinho fam milyan 15 a kowace shekara. Hakan na nufin cewa shi ne na biyu a jerin masu horas da wasanni da aka fi biya da albashi mai yawa.
Kociyan Manchester City, Pep Gordiola ne aka fi biya albashi mai tsoka, har fam milyan 20.
Wadanda ke masa su ne Zinedine Zidane na Real Madrid da Jurgen Klopp na Liverpool.
Ya horas da ‘yan wasan Benfica cikin shekara ta 2000. Daga nan ya yi kakar wasanni daya tsakanin 2001 zuwa 2002 a kungiyar U.D Leiria.
Mourinho ya yi shekara biyu a FC Porto, inda ya lashe kofi shida, ciki har da na Champions League.
A shekaru uku da Mourinho ya yi a Chelsea, tsakanin 2004 zuwa 2007, ya samu nasarar lashe kofi shida, haka a Inter Milan da ya yi kakar wasanni biyu, Jose ya yi nasarar lashe koti biyar tsakanin 2008 da 2010.
Ya haura zuwa kungiyar Real Madrid, inda a can ma ya lashe kofi uku. Mourinho ya koma Chelsea tsakanin 2013 zuwa 2015, har ya lashe kofi biyu.
Sai kuma ya koma Manchester United cikin 2016 zuwa 2018, har ya ci kofi biyu.