Kotu ta soke sabbin masarautun da Ganduje ya kirkiro a Kano

0

Babbar kotu da ke Jihar Kano karkashin mai shari’a Usman Na’Abba, ta soke sabbin manyan masarautu hudu da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya kirkiro.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa ma’sharia Usman Na’Abba ne ya yanke wannan hukunci da aka shigar a Kotu.

Idan ba a manta ba Babbar Kotun Jihar Kano a karkashin jagorancin Mai Shari’a Nasiru Saminu, ta umarci Gwamna Abdullahi Ganduje da Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi cewa kowa ya tsaya matsayin sa, a kan umarcin da kotun ta bayar tun na ranar 10 Ga Mayu.

A waccan ranar dai kotun ta hana a nada sarakunan na Gaya, Bichi, Karaye da kuma Rano.

A yau kuma cikin wata sabuwar kara da wasu masu ikon nada sarki a Kano suka shigar, sun nemi kotu ta haramta nada sabbin sarakunan kuma ta hana kirkiro sabbin masarautun domin sun saba da ka’ida.

Mai Shari’a Sanusi ya ce a dakata tukunna har sai kotu ta yanke hukunci don haka nada sarakunan da kuma ba su sandunan girma duk haramtaccen nadi ne.

Sannan dai idan dai har yanzu ba a manta ba masu ikon zaben sarki a Masarautar Kano su hudu, sun maka Gwamna Abdulahi Umar kotu, bisa rashin amincewar su da kirkiro sabbin masarautu da ya yi.

Hakan ya biyo bayan nada Sarakuna ne wanda yin hakan ya dora sabbin sarakunan a kan su, domin su hakimai ne, ba sararakuna ba ne.

Sauran wadanda aka hada tare da Ganduje aka maka kotu, sun hada da Kakakin Majalisar Jihar Kano, Kwamishinan Shari’a na Kano da kuma sabbin sarakuna hudu da Ganduje ya nada:

Sabbin sarakunan sun hada da Tafida Abubakar Ila, Ibrahim Abdulkadir, Abrahim Abdulkadir ll da kuma Aminu Ado Bayero.

Wadanda suka maka su kotun, su na Manyan Hakiman Kano masu ikon zaben sarki a Kano, wato Madadkin Kano, Hakimin Dawakin Tofa, Yusuf Nabahani; Makaman Kano, Hakimin Wudil, Abdullahi Sarki Ibrahim; Sarkin Dawaki Mai Tuta, Hakimin Gabasawa, Bello Abubakar da kuma Sarkin Ban Kano, Hakimin Dambatta, Muktar Adnan.

Share.

game da Author