Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje zai jagoranci kwamitin da jam’iyyar APC ta kafa domin ya sasanta rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC a Jihar Edo.
An nada kwamitin mutane biyar domin sasanta wannan rikici da ke tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da kuma Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole.
Haka kuma za su duba dalilan da suka sa aka dakatar da shugaban wani bangare na APC, Anslem Ojezua da kuma zarge-zargen da ake yi wa Oshiomhole.
Kamar yadda sanarwar da Sakataren Jam’iyyar APC na Kasa, Lanre Issa-Onilu ta nuna, an dora wa kwamitin nauyin cewa ya binciki asalin wannan sabani tare da mika rahoton binciken sa ga uwar jam’iyya.
“An bukaci kwamitin ya tuntubi dukkan wadanda rikicin ya shafa domin jin bakin kowane bangare.
“ Wannan kuwa wani yunkuri ne da jam’iyyar mu ke yi domin gano yadda za a shawo kan wannan rikici, yadda jam’iyyar mu za ta kara karfi sosai.”
Sauran mambobin kwamitin sun hada da , Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari; tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi; tsohon gwamnan Jihar Barno, kuma sabon sanata, Kashim Shettima da kuma Ahmed Wadada (Secretary).
Kokawar Oshiomhole Da Obaseki
Rikicin da ya tirnike tsakanin Shugaban APC, Adams Oshiomhole da Gwamnan Edo, wanda ya gaje shi, Godwin Obaseki, ya dauki sabon salo, yayin da makon da ya gabata aka dakatar da Oshiomhole da Ojezua.
An dakatar da Oshiomhole bayan shugabannin jam’iyyar 18 daga kananan hukumomi sun amince da sa hannun su wajen nuna rashin amincewa da katsalandan din da Oshiomhole ke yi a harkokin jam’iyyar APC a Edo.
Discussion about this post