HARAJI: Majalisar Dattawa ta amince Buhari ya yi karin haraji

0

A yau Alhamis Majalisar Dattawa ta amince da Kudirin Karin Harajin VAT ya zama doka, inda ta amince da rokon da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi cewa su amince ya maida harajin zuwa kashi 7.5% daga kashi 5%.

Idan Buhari ya sa masa hannu ya zama doka, tunda Majalisar Dattawa ta amince masa, kayayyaki da sauran aikace-aikace za su yi tashi gwaron-zabo, sakamakon harajin da za a kara a kan su.

Sauran dokokin da za a yi wa kwaskwarima kuwa sun hada da Dokar Harajin Ribar Fetur, Dokar Harajin Kwastan, Dokar Harajin Kamfanoni, Dokar Harajin Albashin Ma’aikata, Dokar Harajin Jiki Magayi, wato VAT da sauran su.

Majalisa dai ta amince da a yi wa Dokar Harkokin Kudade kwaskwarima, wadda a cikin sashen dokar har da amincewa a yi karin kudin harajin VAT a ciki.

Sai dai kuma abin mamaki ba a raba wa sanatocin kwafen kudirin dokokin ba, ballantana har zu yi nazarin yadda dokar ta ke ko yadda karin ba zai shafi rayuwar talakawa masu karamin karfi ba.

Yanzu abin da ya rage kawai shi ne Majalisar Tarayya su sa albarka a kan kudirin wanda Majalisar Dattawa ta amince da shi.

Daga nan kuma sai a maida wa Shugaba Buhari, ya rattaba hannu a kai. Shikenan karin harajin jiki-magayi ya tabbata.

Idan ba a manta ba, a ranar da Buhari ya sa hannun amincewa da karin mafi kankantar albashi, ya bayyana cewa babu kudin da gwamnatin tarayya za ta yi karin albashi.

Sai ya shawarci dukkan bangarorin karbar haraji da su bijiro da hanyoyin za gwamnatin tarayya za ta rika samun kudin shiga, domin a rika biyan albashi da su.

Wannan ya sa hukumomin da abin ya shafa, musamman Ma’aikatar Harkokin Kudade, Hukumar Tara Harajin Cikin Gida, Hukumar Kwastan da makamantan su suka bazama wajen karin fito da sabbin haraji.

Share.

game da Author