KASAFIN KUDI: Kaduna ta ware Naira biliyan 42 wa fannin ilimi

0

Kwamishinan ilimi na jihar Kaduna Shehu Makarfi ya bayyana cewa gwamnati ta ware Naira biliya 42 domin inganta fannin ilimi a jihar.

Makarfi ya fadi haka ne ranar Laraba da yake kason fannin ilimi a kasafin kudin shekarar 2020 a zauren majalisar dokoki na jihar.

Ya ce gwamnati za ta yi amfani da Naira biliyan 26 wajen yin manyan aiyukka, Naira biliyan 10 wajen biyan albashin malamai sannan Naira biliyan 12 a kudaden da gwamnati ke kashewa na yau da kullum.

Makarfi ya kuma ce badi gwamnati za ta mai da hankali ne wajen gina hanyoyin cikin gari, gina makarantu,daukan malaman dake kula da walwalan matan dake makarantun sakandare sannan da samar da sauran ababen more rayuwa.

“Gwamati zata gyara makarantun sakandare sama da 500 a jihar ta hanyar inganta gine-ginan makarantun da walwalan malamai.

“Sannan mun kuma an kammala shiri tsaf domin mai da jami’ar jihar Kaduna zuwa wurinta na dindindin dake hanyar Zariya.

“Mun kuma ware isassun kudade domin kammala gina makarantun sakandare da muka fara guda shida sannan muna kokarin mai da makarantun sakandare na jeka ka dawo guda 16 zuwa makarantun kwana.

“Za kuma a ci gaba da shirin ciyar da yaran makaranta tare da kara yawan su sannan za a ci gaba da samar da litattafai da kayan makaranta.

Bayan haka shugaban kwalejin kimiyya da fasaha dake Zariya ‘Nuhu Bamalli, Mohammed Abdullahi ya bayyana cewa kwalejin zata kashe akalla Naira biliyan uku a 2020.

Ya ce daga cikin wadannan kudade makarantar za ta yi amfani da Naira biliyan wajen yin manyan aiyyuka, Naira biliyan 1.7 wajen aiyukkan yau da kullum.

Shugaban hukumar tallafa wa dalibai da kudaden karatu na jihar Hassan Rilwan ya yi kira ga majalisar da tayi gyara a wasu daga cikin dokokin hukumar.

A karshe shugaban kwamitin ilimi na majalisar Yusuf Liman yace kwamitin zata maida hankali wajen ganin ma’aikatan ilimin ta samu yadda take so domin ci gaban jihar.

Share.

game da Author