Yadda wani saurayi ya kule dakin wata mata tana barci ya danne ta – ‘Yan sanda

0

Kakakin rundunar ‘Yan sandan Jihar Ogun Abimbola Oyeyemi, ya sanar wa manema labari a garin Abeokuta yadda wani dan shekara 27 mai suna Adamu Kunle ya lallaba ya kule dakin wata mata ‘yar shekara 38 tana barci ya danne ta.

Ita dai wannan mata da kanta ta garzaya caji ofis ta sanar wa ‘yan sanda abinda Adamu ya aikata.

Oyeyemi ya ce daga jin haka shine jami’ai suka cafke Adamu suka taso keyar sa zuwa caji ofis.

A bayanan da Adamu yayi, ya ce ya dade yana sha’awar wannan mata, kuma ya rika gaya mata amma taki amincewa da bukatar sa. Daga nan ne wata rana tana barci ya yi sanda ya kule dakinta tana barci yayi lalata da ita.

‘Yan sanda sun ce Adamu ya amsa laifin sa sannan ya nemi ayi masa afuwa.

Yanzu dai ‘yan sanda na ci gaba da tsare Adamu har sai an kammala bincike.

Share.

game da Author