Akalla mutane milyan 1,200,000 ne Boko Haram suka yi wa kofar-raggo, a cikin kananan hukumomi biyu a Jihar Barno. Ko’dinatan Majalisar Dinkin Duniya a Najeria a bangaren Ayyukan Agaji, Edward Kallon ne ya bayyana haka.
Kallon ya ce mutanen babu yadda za a yi a kai musu dauki ko agajin gaggawa ko wani tallafi, saboda kusan Boko Haram ne ke cin karen su babu babbaka a yankunan.
Ya kara da cewa tun daga watanni 18 da suka gabata, ma’aikatan jin kai na ta shan fama da hare-haren Boko Haram.
Da ya ke gabatar da takarda a Taron Makamar Tsaro tsakanin Fararen hula da jami’an tsaro, Jami’in na majalisar dinkin duniya ya nanata cewa matsalar da ake fama da ita a yankin Arewa maso Gabas, ba abin a kauda kai daga ita ba ce.
Daga nan sai ya kara bayyana cewa rikicin wanda aka shafe shekaru 10 kenan ana gwabzawa, ya ci rayukan jama sama da 35,000 a jihohin Yobe, Adamawa da Barno.
Don haka ya ce bukatar a karfafa fahimtar juna tsakanin fararen hula da sojoji na da matukar muhimmanci, domin a san halin da yankin ya ke ciki sosai.
Ya ce masu ruwa da tsaki a yankin na Arewa maso Gabas tilas su mike tsaye su sake gina kaunar juna da bai wa juna amana.
Kallon ya kara yin bayanin cewa a yayin da aka shafe shekaru 10 ana fafatawa da Boko Haram, akalla mutane milyan bakwai a yankin su na bukatar agaji matuka.
“A cikin shekaru 10 yakin Boko Haram ya ci rayuka 35,000. Kusan fararen hula 14,000 aka kashe, amma sauran da dama duk sojjin Najeriya ne aka kashe.” Inji shi.
Kallon ya nuna fushi da bacin ran yadda wannan yaki ya ci rakuyan masu ayyukan agaji da yawan gaske.
Ya ce baya ga Boko Haram, sauran masu afka barna kamar ‘yan fashi da kananan barayi duk sun addabi masu gudanar da ayyukan jinkai.
“Ma’aikatan agaji 10 kuma dukkan su ‘yan Najeriya ne aka kashe daga watanni 18 zuwa yau. Har yanzu kuma akwai guda shida da ke rike a hannun ‘yan ta’addar.”
Sai dai kuma ya kara cewa duk wannan abubuwa da ke faruwa ba su kashe guyawun masu kai ayyukan jinkai a yankin ba, duk kuwa a fama da ake yi da karancin masu gudanar da ayyukan jinkai din.
Daga nan sai kuma ya kara nuna damuwar sa cewa yawan kisa da garkuwa da Boko Haram ke yi da masu gudanar da ayyukan jinkai ya rage kumajin da ake da shin a isa ga dimbin jama’ar da ke bukatar agajin gaggawa.
“A cikin wannan shekara da mu ke ciki, akwai wasu jihohi biyu da masu kai ayyukan jinkai da agaji ba su iya shiga.” Inji shi.
Daga nan ya yaba wa sojojin Najeriya dangane da kokarin da suka yi wajen dakile Boko Haram daga fantsamar da ya ci cikin jihohi shida, inda yanzu ya rage saura cikin jihohi uku kadai.
Ya kuma yi kiran cewa ana matukar bukatar gudummawa daga masu kishi, tausayi da jinkai.