JIGAWA: Bakin makiyaya sun fatattaki ‘yan sanda, sun mamaye gonakin manoma

0

Wani gungun makiyaya dauke da makamai sun raunata wani jami’in dan sanda yayin da suka kai wa jerin motocin jami’an hari a Karamar Hukumar Kirikasamma, Jihar Jigawa.

An tura ‘yan sanda a yankin ne, bayan da aka kai wa rundunar ‘yan sandan jihar rahoton cewa wasu bakin makiyaya sun mamaye gonakin jama’a, su na tura dabbobin su na cinye musu amfanin gona tare da sace musu amfanin gona.

Mazuna yankin da suka zanta da wakilin PREMIUM TIMES a ranar Talata, sun tabbatar masa da cewa makiyayan sun ji wa dan sandan raunin ne ta hanyar cilla masa harbi da kibiya.

Kafin sannan kuma a ranar Asabar da ta gabata sun ji wa wasu mazauna karkakar raunuka.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da cewa an garzaya da dan sandan asibitin Nguru da ke cikin Jihar Yobe, wanda ya fi kusa da Kirikasamma ta Jihar Jigawa. Kuma ya na samun sauki.

Kakakin Yada Labarai na Rundunar ‘yan sandan Jigawa, Abdul Jinjiri, ya shaida cewa makiyayan sun kai wa jami’an su hari ne a lokacin da suka je domin su kore su daga gonakin da su ka mamaye.

Wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim Bara’u, ya shaida wa wakilinmu cewa makiyayan sun kafa sansani a cikin dajin Iyo da Gishinawa a tsallaken kogi.

Wannan kuwa ya sa akwai wahalar gaske a iya zuwa a cim musu, domin ko jami’an tsaro sun kasa tsallakawa zuwa wajen su domin su fatattake su.

Cikin makon da ya gabata, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda al’ummar yankin Karamar Hukumar Miga cikin Jihar Jigawa, su na cikin halin zaman zullumin kwararar bakin makiyaya, wadanda aka yi zargin cewa kuma dauke su ke da muggan makamai tare da dabbobin na su.

An kuma samu rahoton cewa makiyayan sun banka dabbobin su cikin gonakin shinkafa da na dawa, inda suka lalata tare da cinye amfanin gonaki 18.

Sakataren mulki na Karamar Hukumar Miga, Kawu Magaji ya tabbatar da wannan rahoto, inda kuma ya kara da cewa abin damuwa ne matuka. Ya ce makiyayan sun mamaye yankin Miga ne, bayan sun gudo daga yankin Hadejia, inda suka yi rikici tsakanin su da manoman yankin.

Ana zargin wadannan bakin makiyaya daga Jamhuriyar Nijar su ka kwararo cikin Jihar Jigawa.

An kuma ce an tura jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda da sauran su domin su shawo kan makiyayan tare da kauce ci gaba da barnata amfanin gona da kuma hana barkewar rikici.

Hakimin Miga, Mohammed Garba ya tabbatar da wannan hali da ake ciki, wanda ya ce al’ummar Masarautar Miga na zaman dar-dar.

Share.

game da Author