‘Yan sanda sun cafke wani dan kasuwa da ya zama likitan karfi da ya ji a Adamawa

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana cewa ta cafke wani likitan karya mai suna Gambo Adamu a Modire-Yolde-Pate dake karamar hukumar Yola ta kudu.

Kakakin rundunar Sulaiman Nguroje ya sanar da haka da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar a Yola.

Ya ce rundunar ta cafke Gambo ne bayan tona asirinsa da wasu suka yi sannan da binciken kwakwaf da rundunar ta yi.

Nguroje yace sakamakon binciken da suka yi ya nuna cewa tun farko Adamu dan kasuwa ne wanda ya shahara a siyar da magunguna kawai. Bayan dan wani lokaci kawai sai ya rikida ya zama likitan karfi da yaji.

Saboda samun wuri wannan Likita, Gambo har kwantar da marasa lafiya yake yi a gidan sa dake da dakuna uku, kawai yana dirka wa mutane maganin da ya ga dama da allurai.

Nguroje ya ce Adamu na nan tsare a kurkuku sannan har an rufe wannan asibiti dake yake duba marasa lafiya a ciki.

Ya ce yan sanda sun da kungiyar likitocin Najeriya reshen jihar (NMA) sannan da gwamnatin jihar sun fara gudanar da bincike akai domin gurfanar da Gambo a Kotu.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne gwamnan jihar Ahmadu Fintiri ya koka kan yadda likitoci da asibitocin karya suka karade jihar.

Fintiri ya ce a dalilin yawan likitoci da asibitocin karya ya sa dole gwamnati ta karkato akalar ta domin ganin an rika cafke ire-iren wadannan mutane dake cin karen su ba babbaka a jihar.

Gwamnan jihar ya yi kira ga ma’aikatar kiwon lafiya da masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya da su hada hannu da gwamnati domin ganin an hana aiyukkan irin wadannan mutane a jihar.

Share.

game da Author