Karamin ministan kiwon lafiya Olorunnimbe Mamora ya bayyana cewa gwamnati ta dauki wasu muhimman matakai domin rage yawan mace-macen jarirai da mata a Najeriya.
Ya fadi haka ne a lokacin da kungiyar ‘Rotary Club International da Rotary Action Group for population and Development (RFPD)’ suka kawo wa ma’aikatan ziyara a Abuja.
Mamora ya ce ya zama dole a samar da manufofi da za su taimaka wajen inganta kiwon lafiyar mata da yara ganin cewa bincike ya nuna cewa mata 576 daga cikin mata 100,000 ne ke mutuwa sannan yara 37 daga cikin 1000 ne ke mutuwa a Najeriya duk shekara.
Ya ce gwamnati a shirye take domin hada hannu da masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiyar kasan domin kawar da wannan matsala.
A karshe kodinata kuma mataimakin shugaban Rotary International farfesa Emmanuel Lufadeju, ya bayyana cewa kungiyar su ta yi shekaru 15 tana mara wa fannin kiwon lafiyar Najeriya baya musamma a bangaren inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana.
Lufadeju ya yi kira ga gwamnati da ta bata izinin shiga cikin kauyukan kasan domin tallafawa kiwon lafiyar mata da yara kanana musamman ta hanyar inganta cibiyoyin kiwon lafiya.
Ya ce sun hada hannu da wasu kwararrun likitoci daga kasar Jamus domin samun nasara a hidimar da suka sa a gaba.
Idan ba a manta ba a watar Satumba ne sakamakon binciken da Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya nuna cewa kasashen dake Nahiyar Afrika sun yi nasarar rage yawan mace-macen yara kanana da mata matuka.
Sakamakon binciken ya nuna cewa a shekarar 2000 adadin yawan yara kanana musamman ‘yan kasa da shekara biyar dake mutuwa ya ragu zuwa rabi.
Sannan yara miliyan 6.2 masu shekaru 15 zuwa kasa ne suka rasu a 2018 wanda daga ciki yara masu shekaru kasa da biyar ne da suka kai miliyan 5.3 ne suka rasu.
Kuma a shekaran 2017 mata sama da 290,000 sun rasu a wajen haihuwa.