Gwamnatin Kano ta ki yarda da rushe sabbin masarautun da kotu ta yi

0

Gwamnatin Jihar Kano ta yi raddi a yau Alhamis, dangane da rushe masarautu hudu da ta kirkiro, wadanda Babbar Kotun Kano ta bayyana haramcin kirkiro su.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Mohammed Garba ya raba wa manema Labarai, ranar Alhamis a Kano, ta ce “duk da wannan hukuncin da kotu ta yanke, gwamnati dai har yanzu ta amince da su, kuma ta na yi musu kallon sarakuna. Sannan kuma za ta ci gaba da mu’amala da su a matsayin sarakuna.”

PREMIUM TIMES ta ruwaito labarin yadda Babbar Kotun Kano ta rutse masarautun hudu da gwamnatin Kano ta kirkiro.

Hakan kuma na nufin cewa ta tsige sabbin Sarakunan Karaya, Gaya, Bichi da Rano, wadanda Gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkiro.

Mai Shari’a Usman Na-Abba ya zartas da cewa dokar da aka yi amfani da ita wajen kirkiro masarautun ba a bi ka’idar da ta dace a bi ba.

Sai dai kuma burbushin daidaikun jama’a sun fito a Kao sun gudanr da zanga-zangar daga kwalaye, masu nuna rashin jin dadin rushe sabbin masarautun da kotu ta yi.
A cikin takardar, Kwamishinan Yada Labarai Garba ya ce su har yanzu gwamnatin su ta na yi wa sarakunan kallo na sarakuna cikakku, ba ta yarda da tsige su da kotu ta yi ba.

Daga nan sai ya kara da cewa Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da nazarinn wannan hukunci domin sanin matakin da za ta dauka a gaba.

Garba ya kara da cewa ya yi mamaki yadda kotun ta yanke hukunci, alhali batun na Majalisar Jiha ne.

Sai dai kuma duk da kin bin umarnin kotu da gwamnatin Jihar Kano ta yi, sanarwar ta yi kira ga jama’a su kwantar da hankulan su, kada su tayar da tarzoma.

Share.

game da Author