ADAMAWA: Gwamna Fintiri ya rage wa Manyan Sakatarori girma

0

Gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa ya rage wa wasu Manyan Sakatarorin ma’aiakatun jihar da yawa girma.

Wannan sanarwa ta fito ne a yau Laraba, kuma aka bayyana cewa rage musu girman ya fara nan take.

An ruwaito cewa Fintiri ya dauki wannan kwakwaran mataki ne bayan da ya karbi Rahoton Kwamitin Tantance Tsarin Ma’aikatan Jihar Adamawa, a Yola, babban birnin jihar.

Daga cikin kakkausan bayanin da sanarwar ke dauke da shi, akwai inda aka bayyana cewa, “Dukkan Manyan Sakatarorin Jihar wadanda mukamin su bai kai Matakin Albashi na 17 ba, an sauke su daga mukaman su na Manyan Sakatarori.

“ Sannan kuma gwamnatin jihar ta soke Ofishin Mataimakin Babban Sakatare, domin wannan ofishi babu hurumin sa a karkashin tsarin dokar Aikin Gwamnati.” Haka Fintiri ya bayyana.

Daga nan sai ya nuna damuwa cewa an wofintar da aikin gwamnati a jihar Adamawa, abin da ya ce shi ba zai amince da haka ba.

Fintiri ya ce ya kama aikin tsaftace tsarin aiki gwamnati kenan a jihar har sai ya tsaftace shi, ya gyara shi kuma ya dawo masa da martabar sa.

Daga nan sai ya bayar da umarnin cire dokar hana daukar ma’aikata da jihar, ya na mai cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar za ta fara daukar masu hazaka aiki a wuraren duk da ake bukatar gudummawar su.

Dangane da rahoton da ya karba daga kwamitin nazarin tsarin aikin gwamnati a jihar kuwa, Fintiri ya ce gwamnati za ta fitar da Farar Takarda domin bayyana duk wani abin da kwamitin ya bankado.

Share.

game da Author