Babbar Kotun Shari’a ta Zamfara ta sake garkame wani jigon dan siyasar Jihar Zamfara a kurkuku. An tura Bello Dankande gidan Yari bisa zargin sa da daukar nauyin ‘yan jagaliyar soshiyal midiya, su na yi wa gwamnatin jihar zagon-kasa.
Dankande wanda wanda shi ma jigo ne a jam’iyyar APC, ya rike mukamin Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu a mulkin Abdul’aziz Yari.
A yau Laraba ne ‘yan sanda suka je gidan sa suka kamo shi, a gidan na sa da ke Gusau, babban birnin jihar.
‘Yan sandan da suka kama Dankande, sun je ne tare da sammacin umarnin kama shi daga kotu.
Sannan kuma ‘yan sanda sun zargi Dankande da laifin hada baki da ‘yan sa kai ana satar shanun Fulani a cikin Karamar Hukumar Bakura.
A kotu dai wanda ake zargin ya musanta dukkan cajin sa da ake yi a gaban alkali.
Sannan kuma lauyan sa mai suna Bello Gusau ya kalubalanci cewa wannan kotun ba ta da hurumin yi wa Dankande hukunci.
Sai dai kuma duk wannan bai hana mai shari’a ba da umarnin a kai Dankande gidan kurkuku a tsare, har zuwa ranar 12 Ga Disamba ba.
Idan ba a manta ba, Gwamna Matawalle ya zargi tsohon gwamna Yari da rura wutar rikice-rikice a duk lokacin da ya shiga jihar Zamfara daga Abuja.
Sannan kuma jiya Talata PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin yadda aka kama dan adawa Ibrahim Danmaliki, shi ma alkalin Babbar Kotun Shari’a da ke Samaru, a Gusau ya tura shi kurkuku, bisa zargin ya na ingiza matasa tayar da hargitsi.
A jiya din dai sai da magoya bayan sa suka cika harabar kotun da aka kai shi su na zanga-zanga.