Wasu mahara dauke da manyan makamai sun sace sarkin kauyen Rubochi, Ibrahim Pada a Abuja ranar Talata.
Shugaban ‘yan sandan kauyen Rubochi Micheal Ada ya sanar da haka ranar Laraba da yake zantawa da manema labarai a Abuja inda ya kara cewa an yi garkuwa da basaraken ne a gidansa dake Rubochi.
“ Da tsakad daren Talata rundunar ta samu labarin sace wannan sarki a fadar sa. Sai dai bayan an sanar damu muka aika da jami’an mu domin su bi sawun wadannan mahara.
Wani mazaunin Robuchi mai suna, Madaki Dogara ya bayyana cewa maharan sun far wa kauyen ne tunda misalin karfe 1:30 na ranar Talata.
Dogara yace maharan na sanye dakayan sojoji a jikinsu sannan suna rike da manyan bidigogi wanda suke rika harbi dashi sama domin tsorata mutanen kauyen.
Ya ce a wajen gudu wasu ‘ya’yan sarkin biyu sun ji mummunar rauni a jikinsu.
A watan Oktoba wasu mahara suka far wa mutane inda suka arce da mutane tara sannan suka harbi wani ma’aikacin hukumar NSCDC a wannan farmakin da suka kai a Peki dake Abuja
Discussion about this post