KURUNKUS: Kotun koli ta yi watsi da Karar Atiku

0

Kotun Koli ta yi watsi da karar da dan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya shigar gabanta yana kalubalantar nasarar da Muhammadu Buhari da jam’iyyar sa APC suka yi a zaben shugaban kasa na 2019.

Idan ba a manta ba Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa ta bayyana cewa Atiku da PDP sun kasa gabatar da kwakkwatan hujjojin da su gamsar da kotun cewa INEC da APC sun tafka magudi a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 Ga Fabrairu, 2019.

Lauyan PDP Mike Ozekhome ne ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa a ranar 30 Ga Oktoba ce Kotun Koli za ta fara sauraren karar.

Atiku da PDP sun ce Kotun Daukaka Kararrakin Zabe ta kwafsa sosai wajen yanke hukuncin da suka ce ta yanzu wasu a karkace, wasu a gicce, wasu kuma a assake. Don haka ba a yi musu adalci ba, kuma ba su gamsu ko amince da hukuncin, wanda suka kira danyen hukunci ba.

Da yake zantawa da manema labarai dan takarar mataimakin shugaban kasa Peter Obi, ya bayyana gamsuwar sa da hukuncin kotun.

” Wannan hukunci da kotun koli ta yanke mun gamsu da shi. Dama can mu je kotu ne domin mu bi hakkin mu sannan mu bi wa talakawa hakkin su na zaben mu da suka yi amma aka hana su abin da suka zaba. Yan zu an akarkare komai muna godewa mutanen Najeriya.

Share.

game da Author