Asusun Tallafawaa kanana Yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya gabatar da sakamakon binciken da ya yi kan yadda ake fama da rashin koshi da ciyar da yara kanana abincin dake gina jiki a Najeriya
A wannan rahoto kuwa, Jihar Kano ce ke kan gaba wajen yawan yara kanana da ba a ciyar da su abinci yadda ya kamata.
Shugaban sashen masana ingancin abinci na UNICEF Simeon Nanama ya gabatar da sakamakon bincike a wani taro da Asusun ta yi a garin Kano ranar Talata.
Nanama yace UNICEF ta yi wannan bincike ne a wasu zababbun kananan hukumomin dake jihar domin gano hanyoyin da za ta bi wajen dakile matsalar.
Kananan hukumomin Bichi da Sumaila ne aka fi smun yara da ke watangaririya cikin su babu abinci sannan kuma duk a kyamushe.
“Tabas idan aka kwatanta adadin yawan yaran dake fama da yunwa, jihar Kano ce a kan gaba. Sai dai kuma wannan matsala bai kai ga yayi wa yaran illa matuka ba.
“ Mun shirya wannan taro ne domin tsaro matakan da za su taimaka mana wajen ganin an kawo kaeshen wannan matsala a jihar.
Daga nan babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Bala Mohammed ya bayyana cewa gabatar da wannan sakamako zai sa gwamnati ta kara zage damtse wajen ganin wannan matsala ya kau a jihar Kwata-kwata.
Idan ba a manta ba a watan Satumban da ya gabata ne mahukunta a Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya suka yi kira ga gwamnatin jihar Taraba da ta gaggauta daukan matakin kawar da matsanancin da yara kanana ke fama da cewa idan ba ayi taka-tsantsan ba za a rasa yara akalla 34,000 a jihar.