KANO: Direba ya kashe dan KAROTA ya tsere

0

Wani mai mota ya bi ta kan jami’in kula da ka’idojin titi, da aka fi sani da KAROTA a Kano, ya kashe shi kuma ya tsere.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da dan KAROTA ya zargi direban da karya ka’idar tuki, kuma daga nan suka shiga tankiya a tsakanin su.

Direban ya bi ta kan dan KAROTA da mota a unguwar Dakata cikin Karamar Hukumar Nasarawa, lokacin da ya tsuguna gaban motar zai balle lambar motar.

Jami’in KAROTA mai suna Tijjani Adamu ya mutu nan take, shi kuma direban ya tsere, har yanzu ba a kama shi ba.

Kakakin yada labarai na Hukumar KAROTA, Nabulisi Abubakar, ya tabbatar da kisan da aka yi wa jami’in na su.

A Kano zai akwai mummunar gaba tsakanin masu tuka motoci da babura da kuma jami’an KAROTA, wadanda ake zargi da wuce-gona-da-iri wajen kokarin tilasta wa masu ababen hawa bin dokokin tuki a kan kwalta.

Sannan kuma ana zargin su da karbar kudade idan sun kama direbobi, ko kuma su kai su ofis a yi musu tara wadda ta kai har kimanin naira 40,000.

Sau da dama su na haddasa hadari idan suka yi kukan-kura suka rike sitiyarin direban da ya yi kokarin tserewa.

A Kano sai ana ci gaba da kuka da su, yayin da ababen hawa ke kara yawa, kuma ake samun yawaitar karya dokokin tuki, a birnin wanda shi ne mafi girma da kuma yawan jama’a a Arewacin Najeriya.

Share.

game da Author