KIWON KIFI: Kebbi ta hada hannu da kungiya domin bunkasa sanar

0

Gwamnatin jihar Kebbi ta hada hannu da kungiyar ‘World Fish Program’ domin bunkasa noman kifi a jihar.

Gwamnan jihar Abubakar Bagudu ya sanar da haka a wani taron da gwamnatin ta yi da wakilan kungiyar a Birnin Kebbi.

Bagudu ya ce gwamnati ta amince da haka ne ganin yadda matsalolin canjin yanayi ya sa ake samun karancin kifi a jihar da kasa baki daya.

“ Sanin kowa ne cewa noman hatsi da kifi ne manyan sana’ar mutanen jihar Kebbi, amma kuma yanzu ana samun matsala sosai a dalilin canjin yanayi da ake samu a duniya.

“ Wannan canji yanayin ya afka wa kogin Matan fada da a yanzu haka kogin na ta kafewa.

Bagudu ya ce gwamnati na kokarin ganin ta samar da mafita da ganin kogin ya dawo da ruwan sa domin manoman jihar.

Ya ce kwararrun ma’aikatan kungiyar ‘World Fish Program’ za su hada karfi da karfe da manoman kifin jihar domin ganin an samu ci gaba a wannan bangare.

Bagudu ya ce gwamnatinsa za ta fi bada karfi wajen inganta rayuwan mutane a jihar domin kubutar da su daga kangin tallauci.

A karshe kodinatan kungiyar Harrison Charo yace kungiyar za ta mara wa gwamnati baya Dari bisa Dari domin inganta fannin noman kifi a jihar.

Share.

game da Author