Muna rokon gwamnati ta tallafa mana da kayan noman rani a jihar Yobe – Manoman Damaturu

0

Manoman rani a Damaturu jihar Yobe sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta tallafa musu da kayan noman rani domin yin noman rani a sawwake a wannan shekara.

Idan ba a manta ba jihar Yobe na daga cikin jihohin da suka yi fama da matsalar ambaliyar ruwa a daminan bana inda mutane da dama suka rasa gidaje da gonakin su.

A dalilin haka manoman Damaturu suka yi kira ga gwamnati da ta samar musu da kayan noman rani domin su samu su yi noma tunda a lokacin damina ya gagara saboda ambaliya da suka yi ta fama da.

Daya daga cikin manoman Mahamud Sani ya ce ya rasa duka abinda ya shuka a daminan bana saboda ambaliay da suka yi fama da. Sani ya ce idan gwamnati ta agaza musu da injin din ban ruwa, taki, da iri zai taimaka musu matuka.

Usman Bukar ya ce ana ciniki matuka a lokacin rani. Ya ce a wannan lokaci ake noma kayan itatuwa da ganyayyakin marmari. Yace a wannan lokaci ana yin ciniki matuka. “Idan gwamnati ta taimaka mana zamu maida abinda muka rasa a damuna.”

Manoman sun roki gwamnati da ta gaggauta taimaka musu domin su samu su iya warwarewa daga matsatsin da suka fada a dalilin hasarar da suka yi a damunan bana.

Share.

game da Author