Jami’in kungiya mai zaman kanta ‘Save The Children’ Isah Ibrahim ya bayyana cewa daga shekaran 2016 zuwa 2019 cibiyar kula da mata da yaran da aka ci wa zarafi ya saurari kararraki 662 a jihar Kaduna.
Ibrahim ya fadi haka ne a taron kare hakkin yara da mata da aka yi a garin Zariya wanda Hukumar wayar da Kai ta kasa (NOA) da asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) suka shirya.
Ya ce daga ciki mutane 662 din da aka yi wa fyade ko kuma aka ci zarafinsu 373 aka kwantar da su a asibitin Gwamna Awan dake Nasarawa Kaduna, 104 kuma an kwantar dasu ne a asibitin Sir Patrick Yakowa dake Kafanchan, 114 kuma a asibitin Yusuf Dantsoho dake Tudun-Wada Kaduna sannan 71 a asibitin Gambo Sawaba dake Zariya.
Ibrahim ya ce unguwannin da aka fi ci wa mata mutunci da yi wa kananan yara fyade sun hada da Tudun Wada, Kakuri, Gonin Gora, Rigasa, Rigachikun, Sabon Tasha, Nasarawa, Romi.
Ya yi kira ga gwamnati da ta karfafa dokar kare mutuncin yara da mata domin rage wahalar da ake fama da shi.
Bayan haka Darektan asibitin Sir Patrick Yakowa dake Kafanchan Grace Yohanna ta ce asibiti ta fi samun mata a matsayin mutanen da suka fi yi wa fyade ko kuma aka ci zarafinsu.
“Akan kawo mutane 104 asibitin mu dake fama da irin wadannan matsaloli inda daga ciki 79 mata ne.
Grace ta yaba wa gwamnatin jihar Kaduna bisa kafa irin wannan cibiya da wasu don kula da wadanda aka yi wa fyade a jihar.
Sannan ta yi kira ga mutane da surika gaggawan kai karar wadanda suke aikata haka a ko-ina suka gamu da su.
Lauyan kare hakkin yara kanana na asusun UNICEF Denis Onoise ya yi kira ga iyaye, malaman addini da boko, sarakunan gargajiya da su hada hannu gwamnati domin ganin an kawo karshen wannan matsala.