Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga ‘yan Najeriya attajirai da su duba yiwuwar bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar mai da hankali wajen kirkiro sana’o’I, bunkasa harkokin kasuwanci, cinikayya da gina kasa Najeriya ta hanyar yin amfani da arzikin da Allah yayi wa kasar.
Buhari ya yi wannan kira ne a taron Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa karo ta 25 (NES25) da ake yi a Abuja, a yau Litinin.
Buhari ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da aiki da kamfanoni masu zaman kan su domin bunkasa tattalin arzikin kasar nan da kuma tsara manufofi na ci gaba a Najeriya.
Bayan nan ya yaba da yadda aka gudanar da zabukan 2019, da kuma yadda wadanda basu yi nasara ba suka garzaya kotu domin kai kukan su. Buhari yace hakan nune cewa lallai an samu ci gaba matuka a harkar siyasa da dimokradiyya a kasar nan.
“An sanar da ni cewa taron na wannan shekara zai maida hankali ne wajen tsara hanyoyin da zasu samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya a musamman harkokin Noma, Hako Ma’adinai, Fasaha da Kere-Kere, da kuma kuma ayyukan Komfuta.
“A tattaunawar da muhawarar da kwararru za su yi a wannan taro, ina son in yi kira gareku da ku maida hankali wajen tsara hanyoyin da za a samu nasara ne a harkokin samun ci gaba da bunkasa tattalin arzikin kasa ta yadda Najeriya zata amfana da su.
Bayan haka Buhari ya yi tsokaci akan nasarorin da aka samu a siyasar Najeriya da zabukan 2019.
“An yi zabuka kuma an kamala lafiya, Najeriya ta nuna wa duniya cewa zata iya zaben shugabanninta batare da an samu matsala ba. Duk da dai an dan samu ‘yan matsaloli, ‘yan Najeriya sun yi zabuka cikin kwanciyan hankali da lumana.
“Mun ga yadda wadanda suka fadi zabuka suka garzaya kotu, maimakon yadda ada zaka ga an barke da rikice-rikice.
“Tun a can farko, Jam’iyyar mu ta APC ta fayyace manufofin ta karara ga ‘yan Najeriya, da suka hada da samar da ayyukan yi ga dimbin matasan mu, kakkafa matakai da manufofi masu inganci domin ci gaba a kasar nan.
“Sai dai kash wasu da dama basu fahimci abinda muke nufi da haka ba wasu na ganin.
“Najeriya kasa ce da ke da al’umma kusan miliyan 200 a cikin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja. Mafi yawan arzikin kasar ya na dankare ne a wasu jihohin da basu wuce hudu ko biyar ba tare da babban birnin tarayya. Wasu daga cikin attajiran kasar nan na zaune a cikin wannan dakin kuma sun sani.
“A haka kenan jihohi 31 dake da mutane akalla miliyan 150 na zaman hannu baka hannu akushe ne da ya sa a yanzu kasa ke ta fama da matsalolin tsaro da yaki ci yaki cinyewa. Hakan yasa kasashen da ke kewaye da Najeriya na fama da irin wadannan matsaloli.
Buhari ya ce gwamnatin sa zata maida hankali wajen ganin an tsara manufofin da zasu inganta tattalin arzikin kasar nan da kuma samar wa mutane sana’o’I da inganta zamantakewa a tsakanin mutanen Najeriya da tsaro.