Masu garkuwa da mutane a jihar Katsina sun sako mutane 14 dake tsare a hannun su.
Bayanai sun nuna cewa wadannan mutane sai da suka shafe tsawon kwanaki 44 a hannun masu garkuwan a dajin Dansandu.
Mutanen da aka sako sun hada mata 13, karamin yaro da sabon jariri daya wanda aka haifa washe garin da za a sako su.
Mai taimaka wa gwamnan jihar kan harkokin yada labarai Abdu Labaran ya ce an danka wadannan mutane a hannun shugaban riko na karamar hukumar Jibiya, Haruna wanda shi kuma ya danka su ga gwamnan jihar Aminu Masari ranar Lahadi da rana.
Wata mata cikin wadanda aka sako mai suna Murja ta bayyana cewa masu garkuwan na basu abinci sau biyu a rana ” sannan sukan yi barazanar kashe mu idan ‘yan uwan su basu kawo kudin fansan suba.”
“Masu garkuwa da mutanen sun ajiye mu ne a wani sansani a dajin da a wannan lokaci adadin yawan mu ya kai 150. Sai dai a hankali, a hankali muke ta raguwa har muka zama mu 14.
Gwamnati ta ce za ta mai da hankalin wajen ganin zaman lafiya ya dawo dirshan a jihar.
Labaran ya kara da cewa gwamnati za kuma ta zauna da gwamnatin jihar Zamfara da kasar Nijar domin a samu yadda za a ci gaba da dakile ayyukan wadannan yan ta’addan.
Idan ba a manta ba a watan Satumba ne wakilan mahara suka sako wasu ‘yan mata 9 da yaro 1 da suka yi garkuwa da su, bayan an sace su daga Ruma, cikin Karamar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina.
An sake su ne a ci gaba da mutunta yarjejeniyar da aka kulla tsakanin ‘yan bindiga da gwamnatin jihar Katsina a karkashin Gwamna Aminu Masari.
Wadanda aka sakin sun bayyana cewa sun shafe kwanaki 32 a hannun ‘yan bindiga kafin gwamnati ta tattauna batun amincewa a sako su.
Sun bayyana cewa an rika ba su abinci daidai gwargwado, sannan kuma sun yi ikirarin cewa babu wadda ‘yan bindigar suka yi lalata da ita a cikin su.