Ministan Kwadago Chris Ngige, ya tabbatar da cewa wata kungiyar malaman jami’o’i, mai suna CONUA, ta mika takardar neman amincewar mallakar rajistar kungiya a ofishin sa.
Wadanda suka kafa kungiyar dai sun balle ne daga cikin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU).
Ngige ya ce tun cikin watan Afrilu masu neman kafa kungiyar suka kai takardar a ma’aikatar sa. Amma ba a kai ga yi ma ta rajista ba tukunna.
Ya ce ya sa a kafa kwamiti domin a duba abin da dokar kasa ta gindaya dangane da kafa kungiyoyi tukunna.
CONUA ta fara bayyana ne daga Jami’ar Obafemi Awolowo, daga nan kuma tuni ta fara samun goyon baya daga jami’o’i.
Kodinata na kungiyar mai suna CONUA, Niyi Ismaheel, ya ce sun yi tunanin kafa kungiyar domin a samu zaman lafiya a jami’o’in kasar nan.
Ya ce yawan tafiya yajin aiki da ake yi ya na gurgunta karatu sosai, kuma ya na kawo jinkirin shekara da shekaru ga dalibai kafin su kammala digiri.
Ismaheel ya ce wannan sabuwar kungiyar malaman jami’a, idan aka kafa ta, za ta fito sa sabbin matakai da dabarun neman biya wa malaman jami’a hakkin su, ba tare da tafiya yajin aiki.
Kokarin jin ta bakin Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU, Biodun Ogunbiyi ya ki cewa komai dangane da yunkurin da wasu ke yi domin ballewa daga ASUU.
Discussion about this post