HARAJIN NAIRA MILIYAN 175: Gwamnatin Kaduna ta garkame harabar Bankin Access uku

0

Hukumar Karbar Haraji dole ta jihar Kaduna ta garkame harabar bankin Access uku da ke cikin garin Kaduna.

Wadanda aka rufe sun hada da bankin daki Titin Ahmadu Bello, Isa Kaita da wanda yake titin Bida duk a cikin garin Kaduna.

Lauyan hukumar KDIRS Francis Kozah ya bayyana cewa tun a shekarun baya ne suka sanar wa bankin cewa jihar Kaduna na bin su kudin haraji har naira miliyan 175.

” Amma duk da kokarin a samu a cimma matsaya game da yadda za a biya wannan haraji suka yi wa gwamnati kunnen uwar shegu. A dalilin haka hukumar ta dauki matakin rufe wasu daga cikin ofisoshin bankin har sai sun biya kuadaden da ake bin su. Sannan kuma ma koda sun biya wannan kudi sai sun biya kudin wahalar kulle harabar bankunan da gwamnati ta yi.

Ya ce bankin za ta biya naira 250,000.

Shugaban hukumar Zaid Abubakar ya ce gwanatin jihar ba za ta daga wa kowa kafa ba a jihar yana mai cewa duk wani mai sana’a ko mai mallakin kamfani da manya-manyan ofisoshi a jihar ya tabbata ya ko su tabbata sun garzaya sun biya bashin aharajin da jihar ke bin su ko kuma su kuka da kansu.

” Gwamnati ba za ta zuba ida tana ganin mutane na sana’a a jihar sannan basu biyan kudaden haraji. Daga yanzu kowa zai dandana kudar sa, ko ka biya harajin ka ko kuma a mu garkame harabar sana’ar ka da karfin tsiya.

Share.

game da Author