Mun kara Harajin ‘VAT’ don inganta lafiya, ilmi da ayyukan ci gaba – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa an yi karin Harajin Jiki Magayi (VAT) daga kashi 5% zuwa kashi 7.5% domin a yi wa jama’a ayyukan inganta kiwon lafiya, ilmi da ayyukan raya kasa.

Buhari ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke gabatar wa Majalisar Tarayya Kasafin Kudin 2020, a ranar Talata.

An dai kara harajin VAT har kashi 50 bisa 100. Sai dai kuma a lokacin an bayyana cewa an yi karin VAT din ne domin a samu kudaden da za a rika biyan karin mafi kankantar albashi da su.

Shi kuma Buhari ya wurin jawabin kasafin kudi ya ce za a yi amfani da kudin wajen inganta fannin kiwon lafiya, ilmi da ayyukan raya al’umma.

“Wadannan karin kudaden haraji, jihohi da kananan hukumomi ne za a rika bai wa har kaso 85%. Domin su rika gudanar da ayyukan raya al’umma wadanda ke musu wahalar aiwatarwa, saboda karancin kudade.

Cikin watan Afrilu Shugaba Buhari ya sa wa dokar fara aiki da sabon tsarin karin albashi. Amma har yanzu ba a ce komai a kai ba.

Cikin wadanda suka caccaki karin harajin VAT har da jagoran APC, Bola Tinubu, wanda ya ce idan aka yi karin, talaka ne zai fi ji a bikin sa.

Sai dai kuma gwamnati ta lissafa kayan abinci da akasari talaka ke amfani da su, a matsayin wadanda ba za a karbi harajin VAT daga gare su ba.

Share.

game da Author