Ambaliya ta ci rayuka 10, ta lalata gidaje 2,714 a Neja

0

An bayyana cewa ambaliya ta yi barnar cin rayuka 10 da lalata gidaje 2,714 a Jihar Neja.

Darakta Janar na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Ibrahim Inga ne ya bayyana haka ranar Laraba.

Inga ya bayyana haka a lokacin da ya ke magana a gaban Majalisar Dokokin Jihar Neja, yayin da ya yi musu bayani a kan ayyukan hukumar a cikin shekarar 2019 da ake ciki.

Ya ce ambaliya ta shafi mutane 21,223 in cikin kananan hukumomi 20, inda garuruwa 123 suka fuskanci ambaliya.

“Ambaliyar wadda ta fara daga cikin watan Agusta sanadiyyar matsanancin ruwan sama kamar da bakin-kwarya, ta kara yin tsanani saboda kwarar da tumbatsar da koramu da gulabe suka rika yi.

“Kwararar da koramu da gulabe suka rika yi ta haifar da rasa rayuka 10, tare da lalata wasu hanyoyi, gadoji, kwalbatoci da gidaje. Tare kuma da lalata gonaki da amfanin gona masu yawan gaske.

Inda ya ce hukumar sa ta kasa kai agajin da ya kamata a wuraren da ambaliya ya shafa, saboda tun kafin watan Agusta ta kashe kudaden da aka ba ta a kasafin 2019, wato adadin naira milyan 200.

A kan haka ne shugaban hukumar agajin gaggawar ya ce ya mika kokon barar hukumar ga gwamnatin jihar, domin neman kai agaji a wuraren da ambaliyar ta shafa.

Idan ba a manta ba, hukumar kula canjin yanayi ta kasa sai da ta yi garkadin cewa za a fuskanci matsananciyar ambaliya a jihohi 29 na kasar nan, musamman a watan Satumba.

Cikin jihohin da aka bayyana kuwa har da jihar Neja.

Share.

game da Author