Bayan sake shafe sama da sa’o’i bakwai ana ci gaba da zaman tattaunawa tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), an sake tashi baram-baram a safiyar yau Alhamis ba tare da an cimma wata sahihiyar yarjejeniya ba.
Tattaunawar wadda aka fara tun ranar Talata, an kai har yau wayewar safiyar Alhamis ana ci gaba da yi, amma aka tashi ba tare da cimma wata matsaya ba.
Tuni jama’a da dama sun fara yi wa batun karin albashin cewa tatsuniya ce ko kuma shafa labarai shuni. Wasu kuma na ganin kasa cika alkawari ne da gwamnatin APC ta dauka a lokacin kamfen din 2015.
An shafe sama sa sa’o’i takwas ana tattaunawa a jiya Laraba, tun karfe 5 na yamma har zuwa karfe 2:15 na dare.
Sai dai kuma bangarorin biyu sun amince su ci gaba da wannan muhimmin taro a yau Alhamis da karfe 7 na yamma.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Gwamnatin Tarayya ta kasa cimma matsaya ita da Kungiyar Kwadago masu barazanar tafiya yajin aikin game-gari matukar ba a biya musu karin albashin ba.
An dade ana ta kiciniyar tarurrukan neman maslaha. Wanda aka fara jiya Alhamis an fara shi da wuri, domin Ministan Kwadago, Chris Ngege bai isa wurin taron da wuri ba.
Baram-Baram
A lokuta daban-daban da aka rika gudanar da tarukan, sau hudu wakilan Kungiyar Kwadago na ficewa a fusace su na barin wakilan gwamnatin tarayya a dakin taro su kadai.
Sai dai kuma yayin da Ngige ya fito bayan tashi daga taron jiya, ya ce an cimma matsaya a batutuwa da wurare da dama. Ya na fatan idan aka je taron yau Alhamis na karfe 7 na yamma, za a kara cimma yarjejeniya da matsaya kwakkwara.
Ya ce amma har yanzu akwai inda ba a kammala daddalewa ba, saboda akwai mabutuwa masu bukatar a warware su dalla-dalla.
Shi ma Shugaban Kungiyar Kwadago, Ayuba Wamba, ya ce har yanzu kofar tattaunawa a bude ta ke. Ya ce akwai alamun warware dukkan mishkilolin da suka dabaibaye batun karin albashin da ake ta yi wa kwan-gaba-kwan-baya.
Wani babban jami’in da ya halarci zaman tattaunar a shekaranjiya Talata, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa NLC ta dan sauko kasa, ta rage adadin abin da ta nema a yi wa masu matakin albashi na 07 zuwa 14, daga kashi 29 zuwa kashi 25 na albashin su.
Sannan kuma NLC ta amince tare da rage yawan abin da ta nema a rika biyan masu matakin albashi daga na 15 zuwa na 17, a yi masu karin kashi 20 maimakon kashi 25 da ta nema a yi musu.
Sannan kuma ita gwamnatin tarayya ta nuna alamar yi wa masu mataki na 07 zuwa 09 karin kashi 17, yayin da masu mataki na 10 zuwa na 14 kuma a yi musu karin kashi 15 bisa 100.
Su kuma masu matakin albashi na 15 zuwa na 17, za a yi musu karin kashi 12 bisa 100, kamar yadda majitar ta tabbatar wa wannan jarida.
Ya zuwa daren yau dai za a ji yadda za a wanye, ko a cimma matsaya, ko kuma ta-ki-ci-ta-ki-cinyewa.
Discussion about this post