Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sabbin hadimai shida wa Uwargidan sa Aisha Buhari.
Kakakin ofishin matar shugaban kasa, Suleiman Haruna ya bayyana haka ranar Laraba.
Haruna yace wadanda aka nada za su fara aiki ne nan take.
Wadanda aka nada sun hada da:
1 – Dr Mairo Almakura – Hadima ta musamman kar harkokin kungiyar samar da zaman lafiya na matan shugabannin kasashen Afrika (AFLPM)
2 – Muhammed Albishir – Hadima ta musamman kan harkokin kungiyar ci gaban matan shugabannin kasashen Afrika (OAFLAD)
3 – Wole Aboderin – Hadima ta musamman kan harkokin kungiyar kan kungiyoyi masu zaman kansu
4 – Barr. Aiyu Abdullahi – Hadima ta musamman kan harkokin Yada Labarai
5 – Zainab Kazeem – Hadima ta musamman kan harkokin cikin gida da shirya bukukuwa
6 – Funke Adesiyan – Hadima kan harkokin cikin gida da shirya bukukuwa