Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Lagos, ta bayyana ceto wasu ‘yan mata su 19, kowace dauke da ciki a wani gidan da ake tara mata ana dirka musu ciki, bayan sun haihu a sayar da jira-jiran.
Kakakin ‘Yan Sandan Lagos, Bala Ekana na sanar da ‘yan jarida cewa an gano gidan a unguwar Iyawale, cikin yankin Ikotun. Ya kara da cewa matan sun kama daga shekaru 15 zuwa 28.
Ekana ya ce an kamo matan ne, ko kuma an ribbace su an kai su Lagos daga jihohin Rivers, Cross River, Akwai Ibom, Anambra, Abia da Imo. Kuma an kai su ne da niyyar samar musu aikin yi a Lagos.
“Daga nan sai a tsare su, a rika yi musu fyade, ana dirka musu ciki. Idan sun haihu, sai masu harkallar su rika sayar da jariran.”
Babbar dillaliyar mai suna Madam Oluchi ta ari takalmin kare, ta arce. Amma an kama wakilan ta biyu, Happiness Ukwuoma da Aherifat Ipaye.
Bincike ya nuna su na saida jinjiri namiji naira 400,000. Mace jinjira kuma naira 300,000.
An kuma gano ka na nan yara hudu a wurare daban-daban da aka rigaya aka sayar da su.
Za a gurfanar da su kotu da an gama bincike.