AMBALIYA: NEMA ta gargadi mazauna garuruwa 4 su arce ba shiri

0

Hukumar Agajin Gaggawa (NEMA), ta gargadi mazauna wasu garuruwa hudu da ke cikin Jihar Imo da su gaggauta ficewa ba tare da bata lokaci ba.

Wannan gargadin ya fito ne daga bakin Babban Jami’in NEMA mai kula da jihohin Imo da Abia, Evan Ugoh.

Ya ce sanadiyyar gargadin da hukumar nazarin yanayin ambaliya ta NIMET ta yi, akwai yiwuwar barkewar ambaliya a garuruwan Eziorsu, Atiaofu, Orsuenbodo da kuma Ossemotto.

Daga nan ya gargadi mazauna Orashi da ke gefen Kogin Neja cewa su ma a bisa yadda yanayi ya nuna, bai kamata su kara kwantawa barci a garin ba.

“Jama’a kada a shagala. Yanayi ya nuna a fice da gaggawa domin a tsira.”

Mista Ugoh ya kuma shawarci masu gina gidaje su daina gini a hanyar da ruwa ke bi ya na wucewa. Ya ce hakan na cutar da mai gidan da kuma sauran jama’a baki daya.

Kwanan nan ambaliya ta ci gidaje 60 a Jihar Ogun, tare da janyo wa mutane sama da 2000 rasa muhallin su.

Idan za a iya tunawa, farkon wannan wata ne hukumar NIMET ta lissafa jihohi sama da 20 da ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar su fuskanci ambaliya a cikin watan Satumba.

Share.

game da Author