Yadda Jami’an SSS suka yi kaurin suna wajen watsi da umarnin kotu

0

Jami’an Tsaro na Farin Kaya na Najeriya, wato SSS sun yi kaurin suna wajen kin bin umarnin kotu, kamar yadda nazarin PREMIUM TIMES ya nuna.

Wannan hukumar dai an kafa ta ne cikin 1986, a karkashin mulkin Ibrahim Babangida. Ta yi kaurin suna wajen kin bin umarnin kotu, duk kuwa da kakabin da Shugaba Buhari ya ke yawan yi na cewa a bangaren shari’a gwamnatin sa ba za ta ki bin umarnin kotu ba.

Ko cikin watan Satumba din nan, a ranar 23 sai da Buhari ya nanata wannan bayani. Shi ma Babban Cif Jojin Najeriya, Tanko Muhammad ya fadi haka.

WASU DA KOTU TA CE A SAKI, SSS SUKA YI BIRIS

Sambo Dasuki

Shi ne Mashawarcin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan a fannin tsaro.

Duk da hukuncin kotu ya nuna a sake shi ba sau daya ba, kuma masu rajin kare hakkin dan Adam sun matsa lamba a sake shi, har yau Dasuki ya na tsare a hannun gwamnati.

Ko a cikin watan Yuli, 2019, sai da Kotun Daukaka Kara ta bayar da belin sa, amma har yau an yi biris. Ya na hannun SSS a tsare.

Sannan kuma kotu ta umarci gwamnati ta biya shi diyyar naira milyan 5 na tsarewar da aka yi masa, wadda Mai shari’a ya ce tsarewar ta kauce wa sashe na 35 na (6) na Dokar Kasar na.

Ibrahim El-Zakzaky

Ana tsare da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tun cikin watan Disamba, 2015, bayan an kama shi. Daga baya an haramta masa kungiyar sa ta mabiya Shi’a, wato IMN. Sojoji sunnkashe masa sama da mabiya 300. An kuma ruguza dukkan wuraren ibadar mabiyan sa a Zariya.

An zarge su da tare wa Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai hanyar hana shi wucewa zuwa wani taro a Zariya.

Wannan kisan kiyashi da aka yi wa mabiya Shi’a ya fuskanci la’anta daga cikin kasar nan da waje baki daya.

Tun cikin Disamba 2015 ake tsare da shi tare da matar sa, Zeenat a ofishin SSS. Da farko sun shafe tsawon lokaci ba tare da gurfanar da su kotu ba. Daga baya kuma aka gurfanar da su bisa zargin kashe wani soja daya a ranar da sojoji suka bude wa mabiya Shi’a wuta a Zariya.

A cikin 2016, Babbar Kotun Tarayya ta bada umarnin a saki El-Zakzaky, amma hukumar SSS ta yi biris da wannan umarni na kotu.

Mai Shari’a Gabriel Kolawole ya umarci SSS su biya El-Zakzaky diyyar naira milyan 50 saboda tsarewar kwanaki 45 da suka yi masa tun a lokacin.

Sai dai kuma SSS ba su sake shi ba, suka buge da cewa sun tsare shi domin kare lafiyar sa.

An ci gaba da tsare shi har cikin 2018, daga nan kuma aka maka shi wata kotu a Kaduna, aka ci gaba da kakaniyar shari’a.

Majalisar Tarayya ta yi kiran a sake shi, a ranar 10 Ga Yuli, bayan Shugaban Marasa Rinjaye, Ndudi Elumelu ya tashi ya yi jawabi.

Omoyele Sowore

A ranar 24 Ga Satumba, Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya, Taiwo Taiwo ya umarci SSS su saki Omoyele Sowore, bayan da mai gabatar da kara ya bayyana wa kotu cewa ya kammala binciken sa. Ya ce ya kammala binciken da suke yi wa Sowore.

Taiwo ya ce a bada belin Sowore, duk lokacin da za a kira shi kotu, sai ya rika zuwa tare da lauyan sa, Femi Falana.

Kwanaki biyar bayan kotu ta ce a saki Sowore, har yau ba a sake shi ba.

Sannan kuma a yau Litinin an sake gurfanar da shi a kotu, a kan wasu tuhume-tuhume daban da aka bijiro da su a kan sa.

Yan Najeriya da dama na nuna damuwa a kan yadda SSS ke gudanar da aiki a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Musamman a kan batun kin bin umarnin kotu.

Tun a ranar 3 Ga Agusta ake tsare da Sowore, saboda zargin shirya taron #RevolutioNow, wanda gwamnati ta zarge shi da yunkurin kifar da gwamnatin dimokradiyya.

Tuni dai ake ta kirayen a saki Sowore, musamman manyan kungiyoyi da masu rajin kare dimokradiyya da ‘yancin ‘yan Adam.

Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) na daga sahun gaba na masu caccakar SSS ta na cewa abin da ta yi a kasar nan, ba ta wa kanta suna ne kawai.

Ta yi kiran a gaggauta sakin Sowore, wanda ya yi takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019.

Shi ne Shugaban Jaridar Sahara Reporters.

Share.

game da Author