KATSINA: ’Yan bindiga sun kara sakin ‘yan mata 9 da yaro 1

0

Wasu ‘yan bindiga dake kai hare-hare a jihar Katsina da aka bayyana cewa sun tuba, sun saki wasu ‘yan mata 9 da yaro 1 da suka yi garkuwa da su, bayan an sace su daga Ruma, cikin Karamar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina.

An sake su ne a ci gaba da mutunta yarjejeniyar da aka kulla tsakanin ‘yan bindiga da gwamnatin jihar Katsina a karkashin Gwamna Aminu Masari.

Wadanda aka sakin sun bayyana cewa sun shafe kwanaki 32 a hannun ‘yan bindiga kafin gwamnati ta tattauna batun amincewa a sako su.

Sun bayyana cewa an rika ba su abinci daidai gwargwado, sannan kuma sun yi ikirarin cewa babu wadda ‘yan bindigar suka yi lalata da ita a cikin su.

An damka su a hannun Shugaban Riko na Karamar Hukumar Batsari, wanda aka bai wa umarni ya gaggauta kai su asibiti domin duba lafiyar su kafin damka su ga iyayen su.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin jihar ta samu nasarar karbo wadanda ka yi garkuwa da su har mutane 67, tun bayan fara aiki da yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar Katsina da wakilan ‘yan bindiga.

Idan ba a manta ba, jiya Litinin PREMIUM TIMES Hausa ta bada rahoton cewa ’Yan bindigar Katsina sun sake sako mutane 30 da suka yi garkuwa da su. Sun sako su ne a bisa yarjejeniyar da cimma da gwamnatin Jihar Katsina da kuma shugabannin su.

Ranar Lahadi ne suka kai wa Gwamna Masari wadanda suka saki din har cikin Gidan Gwamnati.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wadanda aka saki din an yi garkuwa da su bayan an kama su a Karamar Hukumar Kankara da kuma kauyen Shimfida da ke cikin Karamar Hukumar Jibiya.

Bayan an kama su ne aka yi awon gaba da su a Dajin Dansadau da ke cikin Jihar Zamfara, inda suka shafe makonni da dama a tsare.

Da ya ke wa wadanda aka saki din jawabi, Masari ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da lallashin ‘yan bindigar har sai sun saki dukkan mutanen da suka yi garkuwa da su.

Daga nan sai ya bada umarni a gaggauta kai su asibiti domin a binciki lafiyar su, kafin a mika su ga iyalan su.

Daga daga cikin wadanda aka sako din mai suna Zinatu Sani, ta shaida wa manema labarai cewa daga gidan aure aka sungume ta a yankin Kankara aka gudu da ita da ‘ya’yan ta biyu.

Zinatu cewa ta yi da farko naira milyan 20 masu garkuwar suka nema kafin a sake su. Daga bisani kuma suka nemi naira milyan 6, amma duk ba a samu ba.

“Mun shafe kwanaki 55 mu na kwanciya a fili, babu daki babu wata rumfa. A haka ruwa ke dukan mu. Su na ba mu shinkafa zalla da ruwa da gishiri mu dafa.

Daga nan sai Zinatu Sani ta gode wa Gwamna Masari da yi kokarin da ya kubutar da su.

An dai damka wadanda aka kubutar din ga Shugabannin RIko na Kananan Hukumomin Kankara da Jibiya.

Share.

game da Author