Gwanatin Tarayya ta bayar da kyautar katin waya (sim card) da katin kudin lodin kira ‘recharge card’ da za su rika kira har tsawon watanni biyu ga wadanda suka dawo daga Afrika ta Kudu.
Baya ga wannan kuma, an bayanna cewa an dauki sunayen su domin Bankin Kasuwanci ya shirya yadda zai ba su wani dan lamunin kama sana’ar dogaro da kai a nan Najeriya.
Sannan kuma an ba su dan kudin motar da zai kai su garuruwan su. Amma dai ba a bayyana adadin ko nawa ne aka bai wa kowa ba.
Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa ce ta bayyana haka, kuma ta roki gwamnati da ta samar masu hanya madogara dominn inganta rayuwar su a zaman da za su ci gaba da yi kasar nan.
Ranar Litinin ne ta yi wannan jabawi a taron manema labarai da ta shirya a Abuja.
Dabiri-Erewa ta kara da cewa akwai wasu 319 da ake sa ran isowar su Najeriya daga Afrika ta Kudu a yau Talata.
Daga nan ta kara da cewa yawan wadanda za su dawo, ya dogara ne ga yawan wadanda suka je suka yi rajistar bukatar a dawo da su Najeriya. Kuma inji ta, za a ci gaba da wannan korari na dauko su ana dawowa da su gida, ba dainawa za a yi ba.
Ta ce daga cikin wadanda aka dauko a jirgin farko gar da kananan yara 30, wadanda suka sauka kasar nan a ransar 11 Ga Satumba.
“Za a ba su wani dan lamuni domin kama sana’ar dogaro da kai. Kuma an ba su labar da za su kira domin su ji lokacin da za su je su karbi lamunin.”
“Wadanda suka dawo daga Afrika ta Kudu ba fa masu laifi ba ne, ‘yan Najeriya ne masu aiki tukuru domin na neman na kan su. Sun rasa duk abin da suka mallaka a tsawon shekarun da suka yi a Afrika ta Kudu.
Da aka yi mata tambaya a kan batun neman Afrika ta Kudu ta biya diyyar asarar da ‘yan Najeriya suka yi, sai Dabiri-Eriwa ta ce za ta dauki maganar zuwa ga ofishin minista.
Ta ce shugaban kasa ya umarci Ministan Harkokin Waje ya ci gaba da tatauna wannan batun da takwarorin sa na Afrika ta Kudu.