WHO da EU sun tattauna hanyoyin inganta rigakafi a kasashen Afrika

0

Hukumar tarayyar Turai da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) sun gudanar da taro domin tsara hanyoyin inganta yi wa yara kanana allurar rigakafi a kasashen Afrika.

An yi wannan taro ne a Brussels dake kasar Belgium sannan taron ya tattauna yadda kasashen Afrika za su iya dakile yaduwar cututtuka ta hanyar yi wa yara kanana allurar rigakafi.

A nasu bayanan shugaban hukumar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker da shugaban WHO Tedros Ghebreyesus sun ce rashin sani da camfe-camfe na daga cikin matsalolin dake hana yi wa yara allurar rigakafi a Afrika.

Sun ce a dalilin haka kuwa ya sa wadannan kasashe ke fama da cututtukan da allurar rigakafi zai iya kawar da su.

Wadannan cututtuka sun hada da bakon dauro,sankarau,shan inna,tarin lala da sauran su.

Juncker da Ghebreyesus sun ce inganta yin allurar rigakafi da wayar da kan mutane game da mahimmancin yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafi ne mafita.

Idan ba a manta ba a watan Yuli ne kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ya yi kira ga kasashen duniya da su maida hankali wajen kiyaye yin allurar rigakafi a kasashen su.

Kungiyar ya yi wannan kira ne bayan binciken da ya yi tare da hadin guiwar asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) a 2018.

Sakamakon binciken ya nuna cewa har yanzu akwai akalla yara miliyan 20 da ko ba suyi alluran ba ko kuma ba su yi duka alluran ba.

WHO ta ce cututtukan da ya kamata a fi maida hankali wajen yi wa allurar rigakafin su sun hada da bakon dauro, amai da gudawa da na dafin tsatsa ‘Tetanus’

Share.

game da Author