DIYYAR NAIRA TIRILIYAN 9: Ana zanga-zanga a Abuja

0

Masu zanga-zanga dauke da takardu, kwalaye da gyauton fararen kyallaye masu dauke da rubuce-rubuce suna zanga-zangar nuna kin amincewa da tsatsauran hukuncin diyyar naira tiriliyan 3.2 da kotun Birtaniya ta kakaba wa Najeriya.

An ce hadaddiyar kungiyar kungiyoyin rajin kare hakki ne ta shirya zanga-zangar.

Shugaban Kungiyar, Etuk Williams da kuma Babban Sakatare, Abubakar Ibrahim, sun bayyana wannan biyya a matsayin cin zarafin shari’a da kuma rashin yi wa shari’a biyayya gami da rashin ganin darajar Najeriya.

Sun yi wadannan jawabai ne a harabar ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Najeriya, a Abuja.

Wasu daga cikin rubuce-rubucen da ke a jikin kwalaye da gyauton kallayen sun hada da:

“Gaggan ‘yan harkalla da gwanayen kutunguila na neman ganin bayan Najeriya.”, “Boris Johnson, ka taka wa Kotun Birtaniya birki,” da kuma “Wannan diyya za ta karya Najeriya.”

Daga nan kuma sai masu zanga-zangar suka mika wa jami’an ofishin wasika, kana kuma suka nausa ofishin Jakadancin Ireland da ke Maitam, Abuja, can ma suka ci gaba da zanga zanga.

Wannan diyyar makudan kudade an yanka wa Najeriya biyan su a matsayin karya yarjejeniyar kwangila da ta yi, tsakanin ta da P&ID.

Wannan kwangila dai tun zamanin mulkin Marigayi Umaru Yar’Adua aka bada ta. Amma daga bisani ta zama alakakai, har rikicin ya mirgina zuwa kotun Birtaniya.

An kakaba wa Najeriya biyan diyyar ce saboda kin cika alkawarin da ta yi, inda ta karya jarjejeniyar kwangila. Wannan laifi da aka tuhumi Najeriya da yi, ya haifar da dimbin asara ga kamfanin P&ID.

Kwangila ce ta harkar gina masana’antun sarrafa gas da aka cimma yarjejeniya tun cikin gwamnatin marigayi Umaru ’Yar’Adua, cikin 2010.

An ci Najeriya tarar a karkashin Dokar Haramcin Karya Yarjejeniyar Kwangiloli ta Ingila da Wales, ta 1996, da kuma Dokar Haramcin Karya Yarjejeniyar Cinikayya ta Najeriya, mai lamba: CAP A18 LFN ta shekara ta 2004.

An yanke hukuncin ne bayan Najeriya ta shafe shekaru sama da biyar ta na sakacin kin daukaka kara.

Idan har Najeriya ta kasa yin nasarar shawo kan wannan gagarimar matsala ta hanyar sasantawa ko kuma sa’ar yin nasara idan ta daukaka kara, to za a kwace dukiyar Najeriya da ke bankunan Ingila da Amurka, har kwatankwacin dala bilyan 9, wato naira tiriliyan 3.2 kenan, a damka wa kamfanin P&ID.

Akwai matsaloli da mishkiloli a cikin kwangilar, wadda tsohon Ministan Fetur na zamani Umaru Yar’Adua, Rilwanu Lukman ya sa wa hannu. An sa wa kwangilar hannu a lokacin da Umaru ba shi da lafiya, ya na ta hakilon neman lafiyar sa tsakanin Ingila da Saudiyya.

Kotu ta rattaba hukuncin ne tun cikin 2015, watanni biyu bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki.

Shugaban lokacin Goodluck Jonathan ya bar wa Buhari gadon warware matsalar, saboda har ya sauka lauyoyin Najeriya sun tsaya Turanci, maimakon maida hankali wajen warware matsalar.

Buhari ya yi sakacin rashin nada ministoci kan lokaci, wanda hakan ya sa Najeriya ta rasa ministan shari’a da zai bai wa Buhari shawara cikin gaggawa dangane da yadda za a shawo kan lamarin, kafin kotu ta yanke hukunci.

Wadanda su ke kewaye da Buhari a lokacin, watau fadawan sa ‘yan-ba-ni-na-iya, sun nuna masa cewa matsalar gwamnatin PDP ce.

Duk da cewa a yanzu Najeriya ta farka daga likomon gare da ta ke yi, ta na ta gwagwagwar ganin ta yi nasarar rashin biyan diyyar, duk wanda ya nakalci yadda rigimar ta ke, zai tabbatar da cewa da wahalar gaske dan akuya ya kayar da kura a kokawar tsakiyar dokar jeji.

Share.

game da Author