Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, ya ce duk wanda ya san Yari din ya yi handama, sata, babakere, harkalla, wuru-wuru, ko rub-da-ciki a kan wasu kudi, to don Allah ya tona masa asiri.
Ya ce ko ma wane ne, to ya kawo hujja kwakkwara da za ta gamsar da hukuma, har a hukunta shi.
Yari ya yi wannan karin hasken a ranar Lahadi, a gidan sa da ke Talata Mafara, kusa da Gusau, kan hanyar Sokoto.
Ya yi jawabin ne a lokacin da ya karbi bakunci shugabannin jam’iyyar APC na jihar Zamfara.
“Duk wanda ya ce na kwashi dukiyar gwamnati na maida tawa, ko a kasar nan ko wajen Najeriya, to ya fito da hujja ya tona min asiri.
“A matsayi na na gwamna, aiki na shi ne kashe kudade, kuma abin da na yi kenan, amma a bisa ka’idar ciyar da jihar Zamfara gaba, da kuma amfana wa al’ummar jihar Zamfara.
“A matsayin mu na wadanda suka yi imani, mun san cewa duk abin da ya same mu, to kaddara ce daga Allah. Don haka masu ganin cewa za su iya narkar da mu, ko su karya mu, ko su dankwafar da su, to ba za su nasara a kan mu ba.
Yari ya isa gida Talata Mafara ne bayan ya dawo daga Aikin Hajji ranar Asabar. Ya isa tare da dimbin jami’an tsaro masu yi masa rakiya zuwa gida, tun daga filin saukar jirage na Sokoto.
A gida kuma dandazon magoya bayan jam’iyyar APC sun fito tariyar sa daga ko’ina cikin kananan hukumomin jihar, ciki har da shugaban jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, Lawal Liman.
Discussion about this post