Ba mu yarda da shirin RUGA ba – Kungiyar Kiristoci, CAN

0

Kungiyar kiristocin Najeriya ta gargadi gwamatin tarayya data tabbata ta yi watsi da shirin killace fulani makiyaya a wuri daya wato shirin nan na RUGA.

Shugaban kungiyar Kiristocin Samson Ayokunle, ya bayyana cewa kungiyar a kasarnan bata amince da wannan shiri ba kuma tana gargadin gwamnatin tarayya kada ta kuskura ta ci gaba da wannan shiri.

Idan ba a manta ba a watan Mayu ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da wannan shiri na RUGA. Sai dai kuma tun bayan bayyana wannan kudiri nata aka rika caccakar gwamnatin game da wannan tsari da take so ta yi wa Fulani Makiyaya.

Musamman mazauna yankunan kudancin Najeriya, duk sun tsoki lamirin gwamnati akan wannan shiri.

Daga baya dai gwamnatin tarayya ta bayyana dakatar da shirin.

Kungiyar CAN ta ce gaba daya kiristocin Najeriya basu tare da wannan shiri kuma ba za su goya wa gwamnati baya ba game da shi.

Sauran limaman coci-coci da suka halarci taron kungiyar sun bayyana cewa kiristocin kasarnan na daure tamau wuri daya kuma gaba dayan su suna tare a matsayi guda game da shirin RUGA a kasarnan.

Sai dai kuma wasu jihohi kamarsu Zamfara da Kano, tuni har sun fara share filaye domin kaddamar da shirin a jihohin su.

A jihar Zamfara, gwamnan jihar Bello Matawalle, ya ce za a gina wannan alkarya na Fulani tare da gina asibitoci, makarantu da kasuwanni domin jin dadin makiyayan.

Matawalle yace zai kaddamar da gina wannan alkarya ne a ranar da za a yi bukin cikan gwamnatin sa kwanaki 100.

Share.

game da Author