A raba aure na da Nasiru a dalilin kaurace mini a gado da yake yi – Inji Talatu

0

Talatu Sulaiman mahaifiyar ‘ya’ya bakwai kuma mai shekaru 35 ta maka mijinta Nasiru Sulaiman a kotun Magajin Gari dake jihar Kaduna tana rokon kotun ta raba aurenta da mijinta saboda kaurace mata da yake yi a gado.

Ita dai Talatu mazauniyar Makera ne a Kaduna, ta fadi a kotu cewa mijinta na kaurace mata a gado na tsawon dogon lokaci da hakan tauye mata hakki ne.

Ta kuma kara da cewa ko a gidan da suke zama ma tashin hankali ne domin ya ragwargwabe, da mu da beraye ne ke jigila a dakunan mu sannan ga ‘ya’ya har bakwai. Baya ga haka a kullum tsakanin sa da mu naira 300 ne kacal tun safe har dare.

” Kai hatta makaranta duk ya cire su wai shi baya muradin dansa yayi karatun boko haka duk ya dawo dasu gida. Nine na ke zuwa ina yin aikatau domin samun abin da zamu ci da ‘ya’ya na.

” Hakan ma ya bina da zargin wai ina fira karuwanci ne ba aiki ba.

Talatu ta roki kotu ta raba wannan aure domin ita bata ga amfanin ci gaba da zama da irin wannan miji ba.

Maigidan Talatu, Nasir ya ya karyata kirafe-korafen da matarsa ta fadi a kotu yana mai cewa zuki ta amalle ne sannan kuma ya fayyace wa kotu dalla-dalla abinda yake faruwa.

Na farko dai Nasiru ya ce naira 300 da yake ba matarsa kullum na cefanene domin ya wadata gidan sa da isasshen abinci.

A karshe dai alkalin kotun Murtala Nasiru ya yi kira ga Talatu da Nasiru da su je gida su sassanta kansu.

Za a ci gaba da shari’ar ranar 23 ga watan Satumba.

Share.

game da Author