Kara girman nono da baya na kai ga yin ajalin mace – Likita

0

Wani likita da ya kware a aikin yin fida mai suna Rex Dafiewhare ya yi kira ga mata da su nisanta kansu daga kara girman nono da duwawu ta hanyar yin fida yana cewa yin haka na iya yin ajalin mutum.

Dafiewhare ya yi wannan kira ne da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja a makon da ya gabata.

Ya ce mata da dama musamman a wannan zamani da muke ciki kan so su sauya wani sashe na jikinsu, kamar kara girman nono ko kuma duwawunsu. Sau da yawa mata da ke yin haka kan rasa rayukansu.

Akan fada cikin matsaloli kamar su zuban jini,daskarewan jini,yawan kashe,bugawar zuciya da dai sauran su.

Ya ce domin guje wa irin haka ne likitan ya yi kira ga mata da su gujewa yin haka.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne wasu likitoci suka gargadi mata da su guje wa kara girman nonon su ta hanyar fida saboda matsaloli da akan fada.

Likitocin sun kuma kara da cewa duk macen da ta yi irin wannan fida a nonon ta kan yi fama da matsaloli da suka hada da rashin iya shayar da da nono,kamuwa da cutar dajin dake kama nono da jini,nonon da aka kara wa mace kan fashe, rashin samun isasshen barci, yawan ciwon kai da baya da dai, sauran su.

Share.

game da Author