Sanatan dake wakiltan Kaduna Ta Tsakiya, Mal Uba Sani ya bayyana cewa hukuncin da kotun sauraren Kararrakin zabe ta yanke da ta yi watsi da karar da PDP da dan takaran ta Isah Ashiru ya shigar yana kalubalantar zaben gwamna El-Rufai da aka yi a Kaduna
Idan ba a manta ba, a ranar Litinin ne kotun dake sauraren kararrakin zaben gwamna na jihar ya yanke hukuncin karar da PDP ta shigar.
A hukuncin wanda shugaban kotun wannan zama Ibrahim Aboki ya bayyana cewa karkaf shaidu da korafin da PDP ta mika a gaban kotun basu da inganci kwata-kwata.
Daga nan sai ya yi fatali da karar bisa cewa kotun bata gamsu da hujjojin da PDP da dan takaranta Isah Ashiru suka mika a gabanta ba.
Sai dai kuma bayan yanke wannan hukunci, shugaban jam’iyyar PDP Hassan Hyet ya ce basu basu gamsu da hukunci da kotun ta yanke ba yana mai cewa zasu gana a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar domin daukan matsaya a kai.
Shi ko gwamna El-Rufai ya yabawa wannan hukunci ne inda ya ce zai ci gaba da aiki tukuru domin ci gaban jihar Kaduna.
Sanata Uba Sani da ya halarci zaman kotun ya kara da cewa baya ga yabawa kotun da zai yi yana mai tabbatarwa mutanen jihar Kaduna cewa gwamnatin APC za ta ci gaba aiki tukuru domin ci gaban jihar da kasa baki dayi.
Discussion about this post