Hukumar Tallafa Wa Ci Gaban Kasashe Masu Tasowa ta Amurka, wato USAID, za ta zuba jarin dala milyan 300 domin inganta cinikayyar kayan gona nau’i biyar a wasu jihohi bakwai na kasar nan.
USAID ta za zuba wannan jari ne a karkashin shirin ta Ciyar da Al’umma da za ta yi a jihohi bakwai a Najeriya.
Jakadan Amurka a Najeriya ne, Stuart Symington ya bayyana haka a yau Talata a Abuja, a wani taron Masu Ruwa da Tsakin Zuba Jarin Harkokin Noma.
Wannan shiri da USAID ta bijiro da shi, zai zaburad da ‘yan Najeriya wajen maida hankali ga noma kayan gonar da za a rika cin nomriyar su wajen samun kudaden shiga ta hanyar hada-hadar cinikayyar su.
Hakan kuma inji Symington zai kar saukaka hanyoyin gudanar da tsarin hada-hadar wannan cinikayya a bangaren noma.
“Wannan tsari zai magance kasadar da masu cin bashi ko lamuni ke fuskanta a lokutan da suka ranci kudade a bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade suka maka kudaden wajen harkokin noma.
“Zai saukaka hanyoyin noma amfanin gona masu kawo ci gaba hada-hadar kasuwanci domin gina al’umma da kasa baki daya.”
Jakadan na Amurka, y ace USAID za ta janyo kanana da matsakaitan masana’antu (SMEs) 500 masu harkokin noma domin cin moriyar wannan shirin.
Nau’o’in amfanin gona biyar da za a maida hankali a kan su, sun hada da: shinkafa, masara, waken soya da sauran su.
A za bada fifikon cin moriyar wannan shiri ne a Jihohin Kaduna, Niger, Kebbi, Benuwe, Delta, Ebonyi da Cross River.
USAID za ta yi aiki kafada-da-kafada da gwamnatin Najeriya, masu ruwa da tsaki a harkokin noman kayan tasarifi cinikayya da hukumomin da abin ya shafa.
Wadanda za su ci moriyar shirin sun hada da dillalan kayan gonar, masu zuba jari a harkar, da kuma masu gudanar da harkokin noman.
Cikin wadanda suka halarci taron har da gwamnonin Kebbi da Cross River, Ben Ayade da Atiku Bagudu, wadanda dukkan su suka yi bayani a kan muhimmancin wannan shiri da USAID ta bijiro da shi.
Ayade da Bagudu sun buga misali da yadda ake samun nasara da shirin ‘Anchor Borrowers’ na Babban Bankin Najeriya (CBN), wanda suka ce da nag aba ake gane zurfin ruwa.