Kotu ta kwace asusun bankin da ake zargi na tsohon gwamnan Legas ne, Ambode

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta bada umarnin a kulle kuma a kwace wani asusun ajiya a banki, wanda ake zargin na da alaka da Akinwunmi Ambode, tsohon gwamnan jihar Lagos.

An bada umarnin kwace asusun ne biyo bayan zargin wata badakala naira bilyan 9.9.

Mai Shari’a Chuka Obiozor, ya ce a kulle asusun guda biyu, amma kullewar wucin-gadi, bayan da Hukumar EFCC ta nemi wannan izni daga kotun.

Asusun guda daya ya na a bankin Zenith, daya kuma ya na bankin Access Bank, sai kuma wani a First Monument Bank.

EFCC ta shaida wa kotun cewa an kamfaci naira bilyan 9.9 daga asusun Jihar Legas, aka zabga cikin wani asusu da ke bankin FCMB, wanda aka bude a ranar 17 Ga Satumba, 2018.

EFCC ta kara shaida wa kotu cewa asusun mallakar Adewale Adesanya ne, wanda shi ne babban sakatare a Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati a lokacin Ambode ya na gwamna.

Bayan kulle asusun da kwace shi da EFCC ta nemi kotu ta ba ta izni, ta kuma nemi a gurfanar da Adesanya a kotu domin ya bada ba’asin yadda ya mallaki kudaden.

Kungmi Daniel, daya daga cikin jami’an EFCC masu binciken badakalar , ya kuma gano wasu masu hakkin sa hannu a cikin asusun, wadanda suka rika sa hannu ana karkatar da kudaden bayan an fitar da su daga asusun gwamnatin jihar Lagos.

Bayan da Mai Shari’a ya gama sauraren ba’asi daga lauyan EFCC, Mohammed Abbas, sai ya bada umarnin a hana sake cire ko sisi daga cikin asusun, har sai gaskiya ta bayyana tukunna.

Daga nan sai ya dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 9 Ga Satumba.

Share.

game da Author