DOKAR HANA KIWO: Miyetti Allah ya ta maka Jihar Benuwai Kotun Daukaka Kara

0

Kungiyar Kare Hakkin Fulani Makiyaya da aka fi sani da Miyetti Allah Kautal Hore, ta shigar da kara a Kotun Daukaka Kara ta Kasa, inda ta ki amincewa da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke kan hana kiwo sakaka a Jihar Benuwai.

Miyetti Allah ta ki amincewa da hukucin ne, inda ta garzaya Kotun Daukaka Kara ta Tarayya.

Lauyoyin kungiyar, Aliyu Ahmed da Abdulhamid Mohammed ne suka shigar da karar a madadin Miyetti Allah, su na kalubalantar hukuncin da Mai Shari’a Okon Abang ya yanke a ranar 4 Ga Yuli.

Okong ya jaddada halascin dokar haka kiwo da gwamnatin Jihar Benuwai ta kafa tun a cikin 2017.

Kafa dokar ke da wuya, sai Miyetti Allah ta garzaya kotu, domin neman kotu ta haramta dokar wadda tuni a lokacin har majalisar dokokin jihar Benuwai ta sa mata hannu.

Idan ba a manta ba, cikin makon da ya gabata ne Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya bayyana cewa jihar sa ta ga alfanun kafa dokar hana kiwo, domin hakan ya sa an samu saukin tashe-tashen hankula da kashe-kashe a jihar.

Ya bayyana cewa daga lokacin da aka kafa dokar cikin 2017 zuwa makon da ya gabata, an kama makiyaya 81 da suka karya dokar tare kuma da kama shanu 3,000.

Ya ce duk wadanda aka kama din sai da aka ci su tara kafin su karbi shanun su. Amma kuma ya kara da cewa akwai wadanda ke kurkuku a tsare, da har yanzu ba su kai ga biyan tara su karbi shanun na su ba.

Share.

game da Author