Gwamnatin jihar Zamfara ta tsayar da ranar 2 zuwa 6 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a aza tubalin ginin alkaryar RUGA a jihar da kuma kaddamar da ita kanta wannan katafaren fili da aka kebe domin haka.
Sakataren gwamnatin jihar Bala Maru ya sanar da haka ranar Litini da yake zantawa da manema labarai a garin Gusau.
Maru ya kuma ce a wannan rana ne gwamnatin jihar za ta yi bukin cika kwanaki 100 a kan karagar mulkin jihar Zamfara wanda Bello Matawalle ke jagoranta.
Maru yace a wannan rana gwamnati za ta kaddamar da wannan shiri na RUGA sannan za a raba takin Zamani ga wasu garuruwan Fulani da kuma magunguna gyata.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne gwamnatin jihar Zamfara ta ware hekta 300 domin gina rugagen Fulani a duk mazabu uku dake jihar.
Gwamnan jihar Bello Matawalle wanda ya sanar da haka ya ce ” Asanina tun a da Makiyaya da manoma abokan zama ne. A wannan lokaci ne kiyayya ya fado cikin su inda har ya tsananta. Idan Aka gina rugage, za a samu natsuwa a tsakanin su da ci gaba da zaman lafiya a yankuna da dama a kasar nan sannan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa ba ma jihar Zamfara ba kawai.
Matawalle ya kuma kara da cewa gwamnati za ta gina makarantun firamare, asibitoci domin makiyaya sannan za a gina dam-dam na ruwa domin dabbobin makiyaya a wadannan rugage.