Ba tare da wani kame-kame ba. Bari mu tafi kai tsaye mu ce kusancin al’mmar garin Gomani da Abuja, Babban Birnin Tarayya, bai amfana wa garin da mazaunan sa komai ba.
Duk wata babu to akwai ta a Gomani, kauyen hanyar Yangoji a kan titin Abuja zuwa Lokoja.
Ba su da makaranta, ba su da asibiti, babu ruwa kuma babu wuta da sauran ababen da talaka zai san gwamnati ta damu da kula da rayuwar sa.
Ba su da hanyar kirki, domin idan ka bi da mota say daya tak, sai motar ka ta zazzage. Akwai turakun fal waya a gefen hanya, amma ba a daura musu fal wayar ba. Sai dai turakun kawai a tsaye kamar fatalwa.
A gefen kauyen akwai wani gini da suke kira ‘wurin shan magani’. Amma a gaskiya ya fi kama da matattatar ‘yan kwaya da ‘yan-daba. Mutanen kauyen sun kai 500. Amma gadon kwanciya daya ne a mashaya maganin. Ba wuta kuma babu ruwa. Tirkashi!
Gwamnati ta manta da mu
“Gwamnati ta manta da mu, kai ka ce ba a karkashin Babban Birnin Tarayya mu ke ba.” Haka wata jami’in jiyya ya shaida wa PREMIUM TIMES a Gomani. Kuma ya ce asibitin a karkashin Karamar Hukumar Kwali ya ke.
Shi kan sa ginin ba a kammala shi ba, amma a haka jami’an kiwon lafiya su biyu kacal ke hakilon duba marasa lafiya a cikin sa.
“Duk sun sace kudin. Dubi yadda aka fara gini amma aka yi watsi da shi tun shekara biyar da ta gabata.
Wannan ce irin rayuwar da talakawan Gomani ke ciki. Ba su da wata alaka da attajirai da manyan jami’an gwamnati, sai fa wadanda suka yi babbar sa’ar aikin wanke-wanke da gadi a gudajen attajurai. Su ne kadai ke jin kamshin miya mai dadi da kayan gina jikin masu shan miyar, amma ba al’ummar Gomani ba.
Mazauna garin duk asalin su mazauna cikin Abuja ne kafin ta zama babban birnin Tarayya. Su aka tasa, aka matsa da su a cikin kungurmin jeji, aka gina Abuja.
Wani mai suna Danladi Jeji, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa su mazauna Abuja na asali an maida su marayu.
” Shekaru 43 kenan da kirkiro Abuja, amma mu dai gwamnati ta manta da mu. Akwai ma wani gari mai suna Jigba da ke karkashin yankin Kuje. Gaba daya malamin firamare a kauyen daya ne tal.
Mazauna yankin ba su da ruwan sha. Sai dai matan su da mazan su da yaran su su rika gangarawa Kogin Gurara su na kamfata, su sha su yi wanka. Shi ma din sai sun yi tafiyayya tukunna.
Matsalar Gomani kadan ce idan aka kwatanta ta da matsalar wasu kauyuka da ke kusa da Abuja. Sabon Tunga da Dogon Ruwa ta su matsalar ta kai gargara. Ba su da komai sai sunayen kauyukan kawai. Yaran su ba su zuwa makaranta har sai sun je gona sun dawo.
“Maganar gaskiya mu dai mun hakura. Mun daina wahalar kuka da kai korafi. Saboda mun san jiran-gawon-shanu kawai mu ke yi.” Inji wani jami’i.
Kwalara Mugun Ciwo
A yankunan Bassa, al’umma da ke tsakanin Abaji da Kwali, su ma idan su na bukatar ko da ruwan wanke hanci, sai sun yi tafiyayya zuwa Kogin Gurara, a cikin Jihar Neja. Kauyuka da yawa can su ke gangarawa neman ruwan jika makoshi.
“Mun san ruwan nan gurbatacce ne. Har cutar kwalara ya na haddasawa. Amma ya za mu yi idan ba mu sha ba?”
Su kuwa mazauna kauyen Kutara, sun san dadin Kogin Gurara. Amma fa wani lokaci idan ta baci, har tsine masa su ke yi. Su na amfana da ruwan su sha kuma su yi aikace-aikace. Amma kuma yawa da fadi da zurfin kogin ya hana yaran su samun ilmin zamani.
Malaman firamaren Kutara idan damina ta yi ruwa ya cika makil, ba su zuwa makarantar koyarwa, saboda gudun kada kogi ya ci su. Wani ajin da wakilin mu ya leka, teburi biyu kawai ya gani. Wato kenan sauran daliban duk a kasa su ke zama.
Rayuwar Manoman Yanki
Idan ma ka noma amfanin gona, to ba ka yi bankwana da fatara da talauci ba. Saboda akwai jan aikin yadda za ka kwashi amfanin gonar ka kai kasuwa ka sayar. “Yanzun nan idan ba ka yi aune ba, sai a yi garkuwa da kai da kayan gonar ka gaba daya.
Ko kuma barayin su bari sai ka je ka saida kayan a kasuwa, su buyo ka har gida su yi garkuwa da kai. Ka yi noma kenan, amma ka yi wa wani katin banza wahala. Cikin dare daya ya zo ya tsiyata ka.”
Kusa da Abuja, inda manya ke sharewa su katalle a cikin Maitama da Asokoro, akwai kauyukan da masara galihu suka yi cincirindo, kamar Lugbe. Nyanya, Orozo, Karimo ko Dei-dei. Dukkan su ba su da ruwan famfo, kuma akwai matsalar rashin tsafta da rashin tsara gine-gine barkatai.
Mun tuntubi jami’in kula raya FCDA, Felix Nwankwo, amma ya kasa cewa komai.
Discussion about this post