Gwamnatin jihar Kaduna za ta fara biyan ma’aikatan jihar da tsarin mafi kankantar albashi da gwamnatin tarayya ta amince da shi daga watan Satumba.
A wata takarda da mai ba gwamna Nasir El-Rufa’I shawara kan harkokin yada labarai Muyiwa Adekeye ya raba wa manema labarai ya ce gwamnatin El-Rufai ta amince ta fara biyan albashi da haka domin a dadadawa ma’aikatan jihar rai.
“Kafin mu dauki wannan mataki sai da muka duba yawan kudaden harajin da muke samu sannan muka tara da kuma yawan kudaden da muke samu daga gwamnatin tarayya sannan muka ga zamu iya biyan haka a duk wata.
“A yanzu haka gwamnati zata rika kashe akalla naira biliyan 3.759 maimakon naira biliyan 2.827 da take biyan ma’aikatan jihar a duk wata.
“Wannan tsarin ya sa gwamnati ta yi wa kananan ma’aikata karin albashi da alawus na kashi 67 bisa 100, manyan ma’aikata daga mataki 10 zuwa 14 sun samu karin albashi da alawus na kashi 60 bisa 100.