Mahara sun kashe mutane hudu a Katsina

0

Rundunar ‘Yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kisan wasu mutane hudu da mahara suka yi a jihar.

A takarda da rundunar ta raba wa manema labarai ranar Litini a garin Katsina jami’in hulda da jama’a na rundunar Anas Gezawa ya bayyana cewa wannan abin tashin hankali ya faru ne kauyen Tsayau dake karamar hukumar Jibia a daren lahadi.

Gezawa ya ce maharan sun kashe mutane hudu a wannan kauye sannan sun sace shanu da dama.

“Ganin haka ya faru sai wasu matasa majiya karfi suka hadu suka bi sawun wadannan mahara cikin daji.

“Maharan sun gudu amma matasan sun sami nasarar dawo da dabobin da aka sace daga kauyen su.

Ya yi kira ga mazauna jihar da su gujewa daukan doka a hannun su sannan su hada hannu da jami’an tsaro domin ganin an kawar da aiyukkan ‘Yan ta’adda a fadin jihar.

Idan ba a manta ba a watan Mayu ne wasu mahara suka kashe manoma 18 a kauyen ‘Yargamji dake karamar hukumar Batsari.

A dalilin haka matasan kauyen suka fusata suka gudanar da zanga-zanga bayan ‘yan sanda sun kwaso gawar wadannan manoma sun zube su a kofar fadan dakacen Batsari, Tukur Mu’azu Ruma.

Daga kofar fadan dakacen Batsari wadannan matasa sun yi tattakiya sun je fadar sarkin Katsina sannan suka zarce zuwa fadar gwamnati.

Share.

game da Author