A jihar Benuwai ne kotun majistare ta daure wani manomi mai suna Terseer Angbee da ta kama da laifin kashe makwabcin sa don ya sare masa itacen Lemo a gona
Alkalin kotun J.O Ayia ya yi watsi ta rokon sassaucin da wanda tayi kisan ya nema, cewa wai kotun bata da ikon sauraren wannan kara.
Alkali Ayia ya dage shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Agusta.
A zaman kotu ranar, Litini lauyan da ya shigar da karar Godwin Ato ya bayyana wa koru cewa Angbee ya cakawa Mwaikyoga Yandev wuka bisa zargin wai shi Yandev ya sare masa bishiyoyin lemu a gonar sa.
“ Bayan sun yi ta tafka musu akai, Angbee ya fusata ya zaro wuka ya caka wa Yandev a kirji.
Ato ya ce babban dan marigayi Yandev, Torngu Mwaikyoga, ya kawo karar abinda aka yi wa mahaifin sa caji ofis na Buruku.
Ya kuma ce rundunar ‘yan sanda za su ci gaba da gudanar da bincike duk da cewa mailaifi ya amsa laifinsa.